in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Ghana a kasar Sin: Kasar Sin tana kokarin ganin an aiwatar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban
2018-11-06 20:01:29 cri


 

A yayin da ake ci gaba da bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko da aka kaddamar ranar Litinin a birnin Shanghai, wato CIIE a takaice, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da jakadan kasar Ghana a Sin, Ambasada Edward Boateng, inda ya nuna farin-cikinsa game da kokarin kasar Sin na ganin an aiwatar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban a duk fadin duniya.

Ambasada Edward Boateng ya ce, jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin kaddamar da bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko a Shanghai, yana da muhimmanci da ma'ana matuka, saboda raya tattalin arzikin duniya na bukatar kasancewar bangarori daban-daban, haka kuma ya kamata kasashe daban-daban su kara budewa juna kofa. Ambasada Boateng ya ce: "A ganina, wani abu mai muhimmanci shi ne, ya dace a samu tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban. A cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewar, kofar kasar Sin a bude take ga duk duniya, har ma za ta fadada bude kofarta ga kasashe daban-daban, al'amarin da ya karfafa mana gwiwa sosai."

Bikin baje-kolin na wannan karo shi ne irinsa na farko da wata kasa ta shirya wanda ke maida hankali kan harkokin shigar da kayayyaki daga kasashen duniya, al'amarin da ya zama abun tarihi ta fannin harkokin cinikayya. Ambasada Boateng ya ce, bikin CIIE na samar da wata kyakkyawar dama ga kasashen duniya don su shiga kasuwar kasar Sin, inda ya ce: "Duk wata kasa, karama ko babba, mai tasowa ko mai arziki, za ta samu damar fitar da kayayyakinta masu kyau zuwa kasuwar kasar Sin. Tattalin arzikin kasar Sin na bunkasa cikin sauri, kana, Sin ta fi kowace kasa yawan al'umma a duniya, al'amuran da suka baiwa kasashe daban-daban damar su shiga cikin kasuwar kasar."

Ghana ta yi suna sosai wajen fitar da koko, kuma ana yin amfani da kokon kasar don samar da cokuleti da dama a duk fadin duniya. Game da wannan batu, ambasada Boateng ya ce, a halin yanzu, galibin kokon da ake fitarwa daga Ghana zuwa kasashen Turai ne kai-tsaye, daga baya kuma ana sayar da su daga Turai zuwa kasar Sin da ma sauran kasashen duniya. Ambasada ya bayyana cewa: (音响3) "Kamfanonin samar da koko gami da hukumomin dake kula da wannan sana'a na Ghana duk sun zo nan birnin Shanghai, inda muke son kulla zumunci da hadin-gwiwa tare da kamfanonin kasar Sin kai-tsaye, maimakon mu nemi wani na daban mu yi cinikayya. Muna so mu canja irin wannan tsohon tsari na kusan tsawon shekaru sama da 150."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China