in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kara sabon kuzari a kullum domin bunkasa tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa tare
2018-11-05 16:07:51 cri

Da safiyar yau Litinin a birnin Shanghai, aka kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa CIIE karo na farko, inda kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 172, tare da kamfanoni da masana'antu fiye da 3600 suka halarci wannan gagarumin bikin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa. A yayin bikin kaddamarwar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya gabatar da ra'ayoyi uku na ingiza kasashen duniya da su kara yin hadin gwiwa da bude kofofinsu, ya kuma shelanta matakai 5 da kasar Sin za ta dauka na kara bude kofarta ga daukacin duniya. Wadannan ra'ayoyi da matakai tamkar wani sabon kuzari ne mai karfi ga kokarin kare tsarin yin cinikayya maras shinge tsakanin bangarori daban daban, da bunkasa sabon tsarin tattalin arziki mai salon bude kofa, da kuma bunkasa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama da kasar Sin take yi a kullum.

"Matsakaicin mutum ne kawai ke kokarin neman moriya, amma wanda ke da hankali ya kan martaba ka'idojin da kowa ke bi a sabon halin da ake ciki a duniya." Wannan karin maganar al'ummar Sinawa ta bayyana cewa, duk wani mutum, ko wata al'umma, ko wata kasa, dole ne ya martaba ka'idojin da kowa ke bi idan yana son cimma burinsa na yin wani abu. Yanzu, tattalin arzikin duniya yana fuskantar sauye-sauye sosai cikin hali na rashin tabbas, sanin ka'idojin da ake bi a duk duniya shi ne abu mafi muhimmanci.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya takaita cewa, "idan wata kasa ko wata al'umma tana son samun bunkasa, dole ne ta nemi samun ci gaba bisa ka'idojin da ake bi a tarihin ci gaban bil Adama." Ya kuma gabatar da ra'ayoyinsa cewa, yanzu akwai bukatar "yin hadin gwiwa da zaman lafiya" da "bude kofa domin kara yin mu'amala" da kuma "kirkiro sabbin abubuwa." A tsakanin kasa da kasa. Wannan ya bayyana cewa, Shugaba Xi Jinping ya san yadda duniya, musamman kasar Sin suke samun ci gaba. Bugu da kari, Xi Jinping ya jaddada cewa, "Bunkasa tattalin arzikin duniya bai daya babbar ka'ida ce da ake bi kuma ba za a iya canza ta ko kadan ba." "Bude kofa da kuma yin hadin gwiwa muhimmin karfi ne ga ci gaban tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa." Wadannan ra'ayoyin na shugaba Xi za su amfana wa sauran mutane wajen sanin daidai halin da duniya ke ciki halin yanzu. Sabo da haka, ya yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da niyyarsu da kara sabon kuzari, "su tsaya kan matsayi na bude kofa, da yin mu'amala da juna domin fadada damammakin yin hadin gwiwar moriyar juna. Sannan su tsaya kan matsayin kirkiro sabbin abubuwa da kuma hanzarta mayar da tsoffin masana'antu su zama sabbi. Bugu da kari, su tsaya kan ka'idojin yin hakuri da juna, da cimma moriyar juna domin kokarin neman bunkasa tare." Wadannan sabbin shawarwari ne da kasar Sin ta gabatar bisa hakikanin halin da ake ciki a duk duniya domin tinkarar sauye-sauye masu sarkakiya da ake fuskanta a fannin tattalin arzikin kasa da kasa, kana sahihan ra'ayoyi ne da kasar Sin ta gabatar wa duk duniya wajen kokarin neman ci gaba tare da sauran kasashen duniya cikin hadin gwiwa.

An lura cewa, "bude kofa, kirkire-kirkire da hakuri da juna" muhimman kalmomi uku da ya kan furta a cikin jawabinsa, haka kuma fasahohi ne dake bayyana yadda kasar Sin ta aiwatar da manufofin yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga waje cikin shekaru 40 da suka gabata, Bugu da kari, sharudda ne da suka zama dole ga kasar Sin wajen kokarin samun sabon ci gaba mai inganci nan gaba. Musamman kalmar "bude kofa", shugaba Xi ya ce ta kasance kamar "wata alama ce ga sabuwar kasar Sin ta yanzu". Yanzu, kasar Sin wadda ta shiga sabon zamani ta fi bukatar matakan bude kofarta ga waje domin samun ci gaba mai inganci sosai.

Bayan da ya shelanta wasu muhimman matakan kara bude kofarta ga waje a yayin taron tattaunawa na Bo'ao da aka yi a watan Afrilun bana, a yau shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimman matakai 5 daban na ingiza a kara bude kofar kasar Sin ga waje. Wadannan muhimman matakai biyar su ne, sa kaimin shigowa da karin kayayyaki kasar Sin daga waje, kara saukaka matakan shigar baki 'yan kasuwa kasar Sin, samar da yanayin kasuwanci mafi inganci a duniya, sannan kara bude kofofin sabbin yankuna da fannoni ga waje, sai kuma ingiza kara yin hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama ko tsakanin bangarori biyu. Wannan matakai 5 sun yi daidai da bukatu da fata na sauran kasashen duniya, kana matakan a zo a gani ne da kasar Sin za ta dauka domin bunkasa tattalin arzikin duniya bai daya da kuma ci gaban tattalin arzikin duk duniya.

Abin da ya fi mai da hankali shi ne, a cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya alkawarta cewa, kasar Sin za ta bullo da tsarin cin tara, ga wadanda suka karya dokokin kare 'yancin mallakar fasaha na baki 'yan kasuwa, sannan za ta kara inganta aiki da binciken 'yancin mallakar fasaha, domin samar da wani yanayin yin kasuwanci mafi kyau a nan kasar Sin.

Sannan a cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya shelanta cewa, kasar Sin na kokarin kyautata manufarta ta yin gyare-gyare da bude kofarta ga waje a sabbin yankuna, alal misali, tana hanzarta nazarin manufofi da ka'idojin kafa yankin yin cinikayya maras shinge a tsibirin Hainan bisa matakai daban daban, ta yadda lardin zai zama sabon yankin dake bude kofarsa sosai ga waje. Sannan kasar Sin za ta kebe karin yankuna ga shiyyar gwajin yin cinikayya maras shinge ta Shanghai, da dai makamatansu. Wadannan matakai za su zama sabon dandali, inda kasashen waje za su ci moriya sakamakon ci gaban kasar Sin.

Dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar shi ne, tana kuma fatan bude kofarta ga waje bisa matsayi mai inganci sosai shi ne tattalin arzikinta yana da karfi, kuma ba za a iya rushe shi ba. A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya kuma amince a fili cewa, yanzu tattalin arzikin kasar Sin na fuskantar wasu matsaloli, amma a ganinsa, har yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba kamar yadda ake fata, kuma yana sahun gaba a duk duniya.

"Kara samun moriya a sabon zamani" shi ne babban jigon wannan bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin. A nan gaba, kasar Sin ba za ta tsaya ba wajen neman ci gaba bisa manufofinta uku, wato kara bude kofa a matsayi mai inganci, da bunkasa sabon tsarin tattalin arziki mai salon bude kofa, da kuma bunkasa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. Kuma kasar Sin za ta kara yin kokarin ingiza bude kofofinta ga duk duniya gaba daya, da tabbatar da bunkasa tattalin arzikin duniya, da zama wata babbar kasuwa ga kasashen duniya baki daya, ta yadda za ta fi bayar da gudummawarta wajen yin gyare-gyaren matakan aiwatar da harkokin kasa da kasa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China