in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya jagoranci taron karawa juna sani game da batun da ya shafi sassa masu zaman kansu
2018-11-01 21:49:13 cri





Da safiyar yau Alhamis 1 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron karawa juna sani, kan batun da ya shafi sassa masu zaman kansu a nan birnin Beijing, inda shugabannin kamfanoni guda goma suka ba da jawabai daya bayan daya, domin ba da shawara kan yadda za a goyawa ci gaban kamfanoni masu zaman kansu baya a sabon yanayin da ake ciki.

Bayan da ya saurari jawaban, Shugaba Xi Jinping ya ba da wani muhimmin jawabi, inda ya ce, tsarin tattalin arziki mai zaman kai, ya samu ci gaba ne bisa manufofin da JKS ta fitar, bayan da kasar Sin ta bude kofa ga waje, da yin kwaskwarima a gida. Ya kara da cewa, "A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, tsarin tattalin arziki mai zaman kai, ya riga ya zama wani muhimmin kashi, na ci gaban kasarmu, wanda ya samar da dumbin damammakin raya aiki, da samar da guraben aikin yi, da kirkire-kirkiren fasahohi, da ma karuwar yawan haraji. Don haka ya taka muhimmiyar rawa, wajen ci gaban tattalin arziki na kasuwancin kasarmu, mai mulki cikin gurguzu, da kyautata ayyukan gwamnati, da raya kasuwannin ketare. Lallai tattalin arziki mai zaman kai ya ba da babbar gudummawa, wajen ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, wanda ya baiwa duniya mamaki sosai."

Xi Jinping ya jaddada cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin, ta tsaya tsayin daka kan tsarin tattalin arziki tun daga tushe. Ta kuma sa kaimi ga raya tsarin tattalin arziki na mallakar kowa da kowa, wanda bai sabawa amincewa da aikin nuna goyon baya ga tsarin tattalin arziki na masu zaman kansu ba. Ya ce ya kamata a raya tsarin tattalin arziki na mallakar kowa da kowa, da na sassa masu zaman kansu, ba tare da nuna kin amincewa da juna ba.

Xi ya bayyana cewa, "Tattalin arzikin sassa masu zaman kansu, muhimmin kashi ne na tsarin tattalin arzikin kasar Sin, kuma kamfanoni masu zaman kansu, da masu kasuwanci, da mu muna cikin jirgin ruwa daya baki daya. An shigar da tsarin tattalin arziki na tushe, a cikin kundin tsarin mulkin kasa, da ka'idojin jam'iyyar kwaminis ta Sin. Duk wani aikin na nuna shakka ga tsarin, ba zai dace da manufofin jam'iyyar da kasar ba. Dukkan kamfanoni masu zaman kansu, da masu kasuwanci, suna iya yin kokari na samun ci gaba, ba tare da damuwa ba."

Xi yi nuni da cewa, yayin da kasar Sin take kokarin raya tattalin arzikinta, kamata ya yi a kago muhalli mai inganci ga ci gaban tattalin arziki mai zaman kansa, tare kuma da warware matsalolin da kamfanoni masu zaman kansu ke fuskanta, da haka ne kamfanonin za su cika da kuzari, yanzu ya dace a tabbatar da aikin a fannoni shida. Ya ce, "Na farko, rage harajin da kamfanoni masu zaman kansu ke biya, ta hanyar saukaka aikin hukumomin gwamnati da aikin ya shafa. Na biyu, warware matsalolin dake gaban kamfanonin, yayin da suke neman jarin da suke bukata, haka kuma gwamnatin kasar za ta samar da wajibabbun taimako ga wasu kamfanoni, wadanda suke samun ci gaba cikin sauri. Na uku, a samar da muhallin yin gogayya mai inganci, ga kamfanoni masu zaman kansu, ta yadda za a sa kaimi kan su, domin su shiga aikin yin gyare-gyare kan kamfanonin gwamnatin kasar. Na hudu, kyautata hanyar aiwatar da manufar gwamnatin kasar, ta hanyar yin amfani da ma'auni iri guda, domin ciyar da kamfanoni masu zaman kansu gaba yadda ya kamata. Na biyar, a kafa sabuwar hulda tsakanin hukumomin gwamnati, da kamfanoni masu zaman kansu. Ya zama dole kwamitin jami'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da gwamnatoci bisa matakai daban daban, su kara mai da hankali kan wannan bakatu, ta yadda za a kara karfafar zukatan 'yan kasuwa a fadin kasar. Na shida, a kiyaye tsaron lafiyar 'yan kasuwa da dukiyoyinsu, domin tabbatar da gudanar da harkokin kamfanoni masu zaman kansu, tare kuma da samun ci gaba mai dorewa." (Zainab Kande Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China