in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan Kyaututtuka Biyu Da Kasar Sin Ta Baiwa Duniya
2018-11-01 19:01:08 cri

Tun daga ranar 1 ga watan Nuwambar da muke ciki, kasar Sin ta fara aiwatar da wasu sabbin manufofinta na fadada bude kofa ga kasashen waje.

Tun daga ranar 1 ga wata, kasar ta fara rage adadin yawan harajin kwastam da take bugawa wasu hajojin kasashe da ake shigowa da su, wadanda yawan nau'ikan harajin su ya kai 1585. Wannan wani babban mataki ne da gwamnatin kasar Sin ta dauka ta fannin rage harajin kwastam, biyowa bayan rage yawan harajin kwastam da take bugawa wasu hajojin kasashe da take shigowa da su, da yawan nau'ikan harajin da ya kai 1449, tun daga ranar 1 ga watan Yulin bana.

Nan ba da jimawa ba, wato ranar 5 ga wata, a birnin Shanghai, za'a kaddamar da bikin baje-kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin a karo na farko wato bikin CIIE a takaice, inda kamfanoni sama da dubu uku, daga kasashe da yankuna fiye da 130 za su hallara, don fadada harkokin kasuwancin kasa da kasa, da kuma biyan bukatun masu sayayya na kasar Sin, da na sauran wasu kasashen duniya a bangarori daban-daban.

Wannan muhimmin aiki ne da kasar Sin ke yi a fannin sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje. A hakika dai, bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da sabbin manufofin bude kofa ga kasashen waje a dandalin tattaunawa na Asiya na Bo'ao a watan Afrilu na bana, an gabatar da manufofi masu nasaba da hakan, kamar su soke, ko sassauta kayyade jarin waje da ake iya sayen hannayen jari a bankuna da kasuwannin hannayen jari, da kamfanonin inshore, da motoci na kasar Sin, da rage ayoyin kayyade jerin sunayen jarin waje daga 63 zuwa 48, da kyautata hukumar ikon mallakar kasa, wadda za ta sarrafa aikin tabbatar da ikon mallakar kasar, da rage kudin harajin kwastam na motoci da kayayyakin yau da kullum, ta haka kasar Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje. Bikin baje koli na duniya wanda ya shafi shigo da kayayyaki karo na farko da za a bude a wannan wata, wanda za a kara rage kudin harajin kwastam, zai kara sa kaimi ga kasar Sin da ta bude kofa ga kasashen waje, da kawo wa kamfanonin kasa da kasa da jama'arsu karin moriya.

Bikin baje kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko, ya sha bamban da bukukuwan baje kolin kayayyakin shige da fice da kasar ta Sin ta shirya a baya. Kayayyaki sama da dubu biyar ne za su shigo nan kasar Sin a karo na farko. Ban da haka, za a kuma baje kolin sabbin kayayyaki da fasahohi sama da dari a bikin. Ban da haka, cikin kamfanoni da za su halarci bikin har da wadanda suka zo daga kasashen G20, da kasashen BRICS, da kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da ma kasashe sama da 50, da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta ratsa ta cikin su, da kasashe sama da 30 mafiya rashin samun ci gaba. Masu saye da sayarwa daga duk fadin duniya za su gane wa idonsu ci gaban tattalin arziki, da fasaha, da kimiyya na kasa da kasa, tare da fahimtar zarafin da ake da shi a kasuwar kasar Sin.

Abin da ya kamata a lura da shi shi ne, a gun taron dandalin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa na Hongqiao, wanda za a shirya a yayin bikin baje kolin, jami'an gwamnatoci da na kungiyoyin kasa da kasa, da shahararrun masu masana'antu, da kwararru, da masana sama da 2000, wadanda suka fito daga kasashe da yankuna sama da 130, za su tattauna da ba da shawarwari, kan yanayin tattalin arziki da cinikayya da ake ciki a duniya, da nufin kara sabon karfi na inganta cinikayyar duniya, da kuma bude sabon shafi na bude kofa, da samun nasara tare. An kimanta cewa, dandalin tattaunawar zai ba da muryar kiyaye 'yancin cinikayya, da raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa, wanda hakan zai kasance wani muhimmin dandamali, na tattauna manyan batutuwan kasa da kasa.

A jiya Laraba ranar 31 ga watan Oktoba, hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, ta kira taro domin binciken yanayin tattalin arzikin da kasar Sin ke ciki, da ma yadda ake gudanar da aikin tattalin arziki a kasar. Inda ake ganin cewa, a shekarar bana da muke ciki, tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin ya samu bunkasuwa yadda ya kamata, amma akwai rashin tabbas yayin da ake tafiyar da harkokin tattalin arziki, kuma tattalin arzikin kasar ya kara samun tabarbarewa, har ma wasu masana'antu na fama da matukar wahalhalu. Don haka taron ya tsai da kudurin cewa, za a kara bude kofar Sin ga kasashen waje, da ma ci gaba da yin gyare-gyare a gida. Kana za a dora muhimmanci kan neman samun bunkasuwa mai inganci, da sa kaimi ga ci gaban tsare-tsaren tattalin arziki baki daya. Ban da wannan kuma, za a ci gaba da yin amfani da jarin waje yadda ya kamata, da ma kiyaye hakki, da muradun kamfanonin kasashen waje da ke kasar Sin bisa doka.

Wannan matakin da mahukuntan gwamnatin kasar Sin suka dauka, bayan nazarin da suka yi kan yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki, a bayyane take an lura cewa, gwamnatin kasar Sin tana aiwatar da manufar gyaran fuska da bude kofa ga ketare ne, domin dakile kalubaloli iri daban daban, yanzu haka gwamnatin kasar ta dauki matakin rage harajin kwastam bisa babban mataki, kuma za ta shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su daga waje na kasa da kasa karo na farko a birnin Shanghai.

Ganin yadda kasar ta Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje, ko shakka babu kasashen duniya su ma za su samu moriya daga sakamakon da kasar Sin ta samu, yayin da take yin gyaran fuska kan tattalin arziki, tare kuma da bude kofa ga ketare. (Murtala Zainab Lubabatu Bilkisu Kande Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China