in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanoni masu zaman kansu na Sin sun sa kaimi ga yin kirkire-kirkire a kasar
2018-10-30 19:23:30 cri

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake yin rangadin aiki a lardin Guangdong a kwanakin baya, ya jaddada cewa, kamfanoni masu zaman kansu sun samar da gudummawa da dama ga raya tattalin arzikin kasar Sin, suna kuma da kyakkyawar makoma.

Kamfanonin matsakaita da kanana, sun sa kaimi ga yin kirkire-kirkire, da samar da ayyukan yi a kasar Sin, don haka ya kamata kwamitocin jam'iyyar kwaminis ta Sin, da gwamnatocin wuraren kasar, su samar da yanayi mai kyau ga kamfanoni masu zaman kansu, da kamfanoni matsakaita da kanana, a fannonin gabatar da manufofi, da tattara kudi, da yanayin ciniki da sauransu. Kana shugaba Xi yana fatan kamfanonin, za su maida hankali ga ayyukansu, da kara yin kirkire-kirkire, da samun sabon ci gaba.

Wannan ne karo na uku da shugaba Xi Jinping ya yi bayani game da tattalin arzikin kamfanoni masu zaman kansu, da kamfanoni matsakaita da kanana a kasar Sin a cikin wata daya. Batun yin kirkire-kirkire, batu ne da ya fi jawon hankalin shugaban sosai. Wannan ya shaida cewa, yin kirkire-kirkire yana da babbar ma'ana, wajen raya kasar Sin a nan gaba, kana ya nuna kyakkyawan fata ga kamfanoni masu zaman kansu.

Yin kirkire-kirkire ya sa kaimi ga samun ci gaba a kasar ko al'umma, kana shi ne karfin sa kaimi ga samun bunkasuwar kamfanoni. A cikin shekaru 40 da aka bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima, wasu kamfanoni masu zaman kansu, sun jagori da yin kwaskwarima kan fannonin da suke shafar zamantakewar al'ummar kasar, ta hanyar kyautata fasahohi da kayayyaki da tsarin yin ciniki.

Bisa tsarin tattalin arzikin kasar Sin, kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin, ya buga kudin haraji fiye da kashi 50 cikin dari, da yawan GDP nasu ya kai fiye da kashi 60 cikin dari bisa na dukkan kasar Sin, da kuma yawan fasahohin yin kirkire-kirkire da suka samar ya kai fiye da kashi 70 cikin dari bisa na dukkan kasar. Don hakan, shugabannin kasar Sin sun bayar da ra'ayoyinsu na nuna goyon baya ga raya kamfanoni masu zaman kansu, domin wannan zai sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin dukkan kasar Sin.

Yanzu haka dai ana gudanar da juyin juya halin kimiyya da fasaha, haka kuma ana fuskantar sauye-sauyen sana'o'i a fadin duniya, a don haka kasashen duniya suna kara mai da hankali kan karfin kirkire-kirkire yayin da suke kokarin kara karfafa karfin gogayya, saboda karfin kirkire-kirkire zai sa kaimi kan ingancin bunkasuwarsu. Ana iya cewa, kirkire-kirkire yana taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, a ciki, kamfanoni masu zaman kansu, da matsakaita, da kananan kamfanoni a kasar Sin, dake ba da babbar gudumowarsu kan aikin.

A cikin rahoton babban taron wakilan JKS karo na 19 da aka fitar a watan Oktoban bara, an gabatar da manufar gina tsarin tattalin arziki iri na zamani, inda aka jaddada cewa, ya dace a hanzartar ci gaban tsarin sana'o'in dake hada kamfanoni, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da harkar kudi ta zamani da kwararru, ta yadda za a kara karfafawa zuciyar 'yan kasuwa, domin su kafa kamfanoni ta hanyar yin kirkire-kirkire. Yayin taruka biyu na kasar Sin na bana, wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tattaunawa kan rahoton gwamnati, na tawagar wakilan lardin Guangdong, inda ya yi nuni da cewa, kirkire-kirkire ya fi muhimmanci, yayin da ake raya kasa.

Kwanan baya shugaba Xi ya yi rangadin aiki a wasu kamfanoni masu zaman kansu na lardin Guangdong, inda ya ga babban sakamakon da suka samu, bayan da suka fara raya kamfanoninsu ta hanyar yin kirkire-kirkire, a don haka Xi ya nuna fatansa gare su. Hakan ya nuna amincin siyasa da goyon bayan manufar gwamnatin kasar, haka kuma zai sa kaimi ga ci gabansu a nan gaba.

Kana gwamnatin kasar Sin, ta dauki wasu hakikanan matakai, na saukaka ayyukan hukumomin gwamnati, da rage haraji, da rage kudin ajiya a banki da sauransu, duk wadannan za su taimakawa kamfanoni masu zaman kansu, su shiga kasuwa, tare kuma da samun isasshen rancen kudin da suke bukata daga banki. A karshe dai za su taka rawar gani, wajen ciyar da tattalin arzikin kasar Sin gaba yadda ya kamata. Haka kuma za su taka rawar gani kan ci gaban kimiyya da fasaha na bil Adama.(Zainab Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China