in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nau'o'in kayayyaki sama da dubu biyar za su shigo kasar Sin
2018-10-30 14:48:24 cri





Daga ranar 5 zuwa 10 ga wata mai zuwa, za a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na farko a birnin Shanghai na kasar. Wakilin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin mai kula da shawarwari kan cinikayyar kasa da kasa, kana mataimakin ministan kasuwanci na kasar, wanda kuma shi ne shugaban ofishin kula da harkokin shirya bikin baje kolin, Mr. Fu Ziying a yayin da ya yi karin haske game da bikin a jiya Litinin, ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin kaddamar da bikin baje kolin, a yayin da shugabannin siyasa da 'yan kasuwa da suka fito daga kasashe da shiyyoyi 150 za su halarci bikin. Lubabtu na tare da karin haske.

A gun taron manema labarai da aka shirya a wannan rana, Mr. Fu Ziying, wakilin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin mai kula da shawarwari kan cinikayyar kasa da kasa, kana mataimakin ministan kasuwanci na kasar ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya bada shawarar gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin, kuma shi zai halarci bikin kaddamar da bikin baje kolin, ya ce, "Za a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin daga ranar 5 zuwa 10 ga wata mai zuwa, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin kaddamar da shi tare da halartar sauran harkoki na bikin baje kolin. Ya zuwa lokacin, shugabannin siyasa da 'yan kasuwa da suka fito daga kasashe da shiyyoyi na duniya kimanin 150 da wasu jami'an kungiyoyin kasa da kasa za su halarci bikin. A ranar 4 ga wata mai zuwa, shugaba Xi Jinping da uwargidansa za su kira liyafar maraba da baki mahalarta bikin, sai kuma a ranar 5, shugaban zai halarci bikin kaddamar da bikin baje kolin tare da gabatar da jawabi. A yayin bikin baje kolin, shugaba Xi Jinping zai kuma gana da shugabannin kasashe daban daban da suka halarci bikin."

Mr. Fu Ziying ya kuma kara da cewa, bikin baje kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigo da su kasar Sin irinsa na farko ne a duniya da aka shirya da jigon kayayyakin da ake shigo da su daga kasa da kasa, kuma an kasa bikin gida biyu, wato bikin baje kolin harkokin cinikayya da zuba jari da kayayyakin masana'antu, da kuma taron dandalin tattaunawar harkokin cinikayya a tsakanin kasa da kasa. Har wa yau, jami'in ya ce, akwai kasashe 82 da ma kungiyoyin kasa da kasa guda uku da suka kafa rumfunansu a wajen bikin baje koli na wannan karo, a yayin da wasu kasashe 12 sun kuma kafa gidajensu na musamman. "Indonesia da Vietnam da Pakistan da Afirka ta kudu da Masar da Rasha da Burtaniya da Hungary da Jamus da Canada da Brazil da kuma Mexico sun kafa gidajensu na musamman don nuna kayayyakinsu. A matsayinta na kasa mai masaukin baki, kasar Sin ta kafa gidanta, ciki har da rumfunan nune-nunen yankunan Hongkong da Macao da kuma Taiwan. Gidan kasar Sin zai nuna manyan nasarorin da kasar ta samu tun bayan da ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da ma sabon zarafin da kasar ta samarwa duniya bisa ga ci gabanta da kuma shawararta ta "ziri daya da hanya daya".

An kafa wasu gidaje bakwai na nune-nunen kayayyakin masana'antu, kuma kamfanoni sama da 3000 da suka fito daga kasashe sama da 130 za su nuna kayayyakinsu. Ya zuwa lokacin, kayayyaki sama da 5000 za su shigo nan kasar Sin a karo na farko, Fu Ziying ya ce, "Kayayyakin da za a baje kolinsu sun hada da amfanin gona da abinci masu inganci, da kuma na'urorin kiwon lafiya da sabbin magunguna na tinkarar cutar sankara. Bisa ga rajistar 'yan kasuwa, kayayyaki sama da 5000 za su shigo nan kasar Sin karo na farko. Wato ke nan masu sayayya da kamfanoni za su samu damar sayen kayayyaki masu inganci da araha daga kasa da kasa ba tare da zuwan kasashen ba, hakan nan kuma zai biya bukatun gida da kuma sa kaimin ci gaban tattalin arzikin kasar."

Taron dandalin tattaunawar harkokin cinikayya na kasa da kasa shi ma wani muhimmin bangare ne na bikin, wanda kuma zai janyo jami'an gwamnati da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa da ma mashahuran 'yan kasuwa da masana sama da 2000. (Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China