Birnin Shenzhen na kasar Sin, wuri ne da aka fara gwajin manufar yin gyare-gyare a kasar Sin, haka kuma wurin ne da kasar ta fara bude kofarta. Jaridar "The Economist" ta kasar Burtaniya ta taba bayyana birnin kamar haka, "daga cikin yankunan tattalin arziki na musamman sama da dubu hudu na duniya, Shenzhen ya zama misali na azo a gani." A hakika, a cikin shekaru 40 da suka wuce, Shenzhen ya taso ne daga wani karamin kauyen masunta da ke dab da birnin Hong Kong, har ma ya zama wani birni na zamani na kasar Sin, ya zama misali na yin gyare-gyare da bude kofa a kasar ta Sin.
Kalubalen gwaji ko kalubalen zama na farko, wani irin karsashi ne da Sin ta kaga shekaru 40 da suka gabata, domin aiwatar da yin gyare-gyare a cikin gida, da bude kofa ga kasashen waje. Bisa yanayin da ake ciki na raguwar ci gaban tattalin arzikin duniya, da farfado da yaki da dunkulewar tattalin arzikin duniya, da kuma takadamar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, ko kasar Sin za ta iya tinkalar kalubalolin ko a'a, kuma ko za ta iya ci gaba da gudanar da manufar ta yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare ko a'a? Dukkanin wadannan tambayoyi na jawo hankulan kasashen duniya sosai. Kwanan baya hukumar kididdiga ta kasar Sin ta sanar da cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar a tsakanin watannin Yuli zuwa Satumba ya ragu zuwa 6.5%, wato kasar na fuskantar tsanantar matsala wajen samun ci gaba. Amma, saboda daidai irin halin da kasar ke ciki ne, ake iya gano cewa, kasar Sin na da karfi da makoma mai kyau wajen samun ci gaba.
Ga misalin, bisa kididdigar da gwamnati ta bayar, an nuna cewa, a watanni 8 na farkon bana, an kafa sabbin kamfanonin da 'yan kasuwa na kasashen ketare ke zuba jari a kai da yawansu ya kai 9724, wanda ya karu da kaso 186.25% bisa na makamancin lokacin bara. Ba a bullo da alamar janye jari a bakin wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma ba, a maimakon haka, bisa fifikon da birnin ke nuna a fannonin yin kirkire-kirkire ta hanyar kimiyya da fasaha, da samar da kayayyaki, da kwararru, da kuma muhallin gudanar da cinikayya, kana da amfani da dama mai kyau ta bude gadar Hong Kong-Zhuhai-Macau, da babban yankin sashen bakin teku na Guangdong-Hong Kong-Macao, birnin nan na Shenzhen na ci gaba da zama wurin da 'yan kasuwan kasashen ketare suka fi son zuba jari a kai a nan kasar Sin.
Abu mai matukar ban mamaki da birnin Shenzhen ya samu ta fannin neman bunkasuwa, ya shaida irin babban ci gaban da kasar Sin ta samu. Bisa rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, an ce, a farkon rabin shekarar da muke ciki, Sin ta zama kasa ta farko da ta jawo jarin waje a duk fadin duniya, kuma adadin yawan jarin da aka zuba a kasar ya karu da kaso 6%, idan aka kwatanta da adadin da ya zuba a Amurka a makamancin lokacin bara. Har wa yau, alkaluman da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Satumbar bana, adadin yawan jarin wajen da kasar Sin ta yi amfani da shi ya karu da kaso 6.4%, wanda saurin karuwarsa ya kai matsayin koli tun daga shekara ta 2015.
Lardin Guangdong shi ne na farko da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin. Yayin da yake rangadin aiki wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci lardin Guangdong da ya kara fahimtar manufar yin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje a sabon zamanin da muke ciki, da ci gaba da aiwatar da ita daga manyan fannoni.
Manazarta na ganin cewa, muhimman kalaman da Xi Jinping ya yi a yayin ziyararsa a lardin Guangdong, tamkar sabon ma'auni ne ga aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje a sabon zagaye, kana kuma kasar Sin na nan na ci gaba da samar da sabbin abubuwa masu ban al'ajabi ga duk duniya. (Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, Murtala Zhang)