in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta shirya halartar bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin a Shanghai a watan Nuwambar 2018
2018-10-26 09:09:34 cri

A yayin da ake shirin gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin a Shanghai a watan Nuwambar shekarar 2018 a karo na farko, Najeriya na daga cikin kasashen duniya daga nahiyar Afrika da suke da burin halartar wannan gagarumin biki. A nata bangaren, jami'ar yada labarai da hulda da jama'a ta majalisar ciniki da masana'antu ta jihar Legas, Madam Temitope Akintunde, ta ce Najeriya ta yi cikakken shiri don halartar bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin a Shanghai na kasar, wadda a cewarta wata muhimmiyar dama ce da kasar za ta yi amfani da ita wajen haduwa da abokan mu'amalar cinikiyya na kasa da kasa da kuma samun damar tallata kayayyakin da Najeriya ke samarwa ga kasuwannin duniya.

Ta ce, a halin yanzu Najeriya ta yi nisa wajen shirye-shiryen halartar bikin baje kolin wanda ake sa ran kamfanoni sama da 2,800 daga sassan duniya daban-daban za su halarta, ta ce, Najeriya ta tanadi babbar tawagar 'yan kasuwa da jami'an gwamnatoci domin halartar bikin baje kolin, a cewarta, majalisar ciniki da masana'antu ta jihar Legas na daga cikin wadanda za su halarta, a jihar Legas kadai wadda ita ce cibiyar kasuwancin Najeriya akwai kamfanoni masu yawa da za su halarci bikin.

Ta ce: "Daga Najeriya na tabbata muna da babbar tawaga da za ta halarci bikin baje kolin, kuma a majalisar ciniki da masana'ntu ta jihar Legas akwai kamfanoni kimanin guda bakwai da za su halarci bikin, wannan daga majalisar ciniki da zuba jari ta jahar Legas ne kadai, kuma na san muna da sauran tawagogi daga ciki da wajen Legas da za su halarci bikin baje kolin, don haka ina mai tabbatar maka da cewa, Najeriya a shirye take ta halarci wannan mashahurin biki irinsa na farko kuma mafi girma mai cike da tarihi."

Misis Akintunde ta ce, a Najeriya akwai kamfanoni na cikin gida dake samar da kayayyaki irin na gargajiya wadanda za su halarci gagarumin bikin naje kolin Shanghai, domin gabatar da hajojinsu da kuma iri iren ayyukan da suke gudanarwa wanda zai ba su damar samun karbuwa a wajen abokan huldarsu na kasar Sin da sauran kasashen duniya, musamman kamfanonin da suka kware wajen samar da tufafin gargajiya, da kayan kwalliya, da wadanda suka kware a fannin ayyukan yawon bude ido.

Ta ce: "Muna da kamfanoni dake samar da nau'ikan tufafin gargajiya na Afrika wadanda suka kware wajen saka tufafi da rinasu a cikin gida wanda aka fi sani da suna 'Adire' a nan kuma Najeriya, muna da wasu kamfanoni da suka kware wajen sarrafawa da samar da kayayyakin kwalliya da ake samar da su a cikin gida a nan Najeriya, sa'annan muna da kamfanonin da suka kware a fannin ayyukan yawon bude ido wadanda za su halarci wannan bikin baje koli, muna da kamfanoni masu tarin yawa da za su shiga a dama da su a wannan bikin baje kolin."

Game da tambayar da aka yi mata kan cewa ko wane tabbaci take da shi dangane da kayayyakin da ake samarwa ko zai iya samun karbuwa a kasar Sin, sai ta ce:

"Idan har ka duba yanayin sayayya a sassan duniya a yau, akwai wasu nau'ikan kayayyaki wadanda ake iya amfani da su a sassan duniya daban-daban, irin wadannan nau'in tufafin da ake rina su wannan wata fasaha ce da aka fara ta a Najeriya sama da shekaru 100 da suka shude, wannan wani aiki ne da aka gada tun kaka da kakaninmu sun jima suna yinsa, kuma irin hanyar da suke bi wajen aikin yana matukar kayatarwa kuma idan suka kammala kayan, suna da matukar ban sha'awa kuma yana da alaka da abubuwan gargajiya, wannan wani al'amari ne da zai kara fito da Najeriya a idanun kasashen duniya, kuma wannan wani abu ne da muke so mu rungume shi a matsayin wani bangare na al'adunmu wadda muka gada daga kaka da kakanni."

Temitope Akintunde ta ce bikin baje kolin na Shanghai bayan damar da zai baiwa Najeriya wajen nuna al'adun da ta gada daga kaka da kakanninta ga kasashen duniya, hakazalika taron wata muhimmiyar dama ce ga kasar wajen samun damar halartar tarurrukan kulla alakar cinikayya tsakaninta da bangarori daban daban zuwa 'yan kasuwa na kasashen duniya, da kuma samun damar halartar tarurrukan tsakanin 'yan kasuwa da wakilan gwamnatocin kasashe daban daban domin bude kofa da tallata hajoji ga sassa daban daban na duniya, da bada damar gudanar da cinikayya tsakanin bangarori daban daban da kuma samun damammaki domin Najeriya ta gabatar da irin abubuwan da za ta iya sayarwa a kasuwannin duniya ta fuskoki biyu, wato ta saya kuma ta sayar da kayayyaki.(Ahmad Inuwa Fagam/Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China