in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ayar Doka Ta 301 Ta Bayyana Niyyar Amurka Ta Hana Ci Gaban Kasar Sin
2018-10-25 19:29:35 cri
Kwanan nan ne wata kungiya wadda gwamnatocin kasa da kasa da wasu kasashe masu tasowa kimanin 50 suka kafa, mai suna "The South Center" wato cibiyar kasashe masu tasowa a hausance, ta bayar da wani rahoto mai taken "Me ya sa ake cewa ayar doka ta 301 ta kasar Amurka ba ta bisa doka kuma kuskure ce", rahoton da ya sake jawo hankalin duniya kan wannan ayar doka da ake cece-ku-ce a kai.

An dai kafa cibiyar The South Center ne a shekarar 1995, cibiyar da ta ke dukufa a kan hadin kan kasashe masu tasowa, da kuma karfafa fahimtar juna a tsakanin kasashe maso tasowa, da kasashe masu ci gaba, bisa ga tushen zaman daidaito. Wannan rahoto da kungiyar ta samar, ya kunshi shafuka kusan 50 da kuma babi bakwai, wadanda suka yi bayani a kan tarihin tanadi, da kuma zargin da Amurka ta yi wa kasar Sin, da ma kuskuren da Amurka ta yi kan batun.

Ayar dokar ta 301, ta fito ne daga dokar cinikayya ta shekarar 1974 da kasar Amurka ta tsara, ita ce muhimmin abu da 'yan cinikayyar kasar Amurka ke amfani da shi wajen fitar da kayayyakinsu. Ga misali, a shekarar 1975, bisa dokar 'yan cinikayyar dake samar da kwai sun taba bukatar gwamnatin Ford, da ta yi bincike kan ayyukan da kasar Canada ta yi musu ta hanyar kayyade kason kayayyakin da ake shigowa da su. A shekarar 1976, bisa wannan doka kwamitin kula da harkokin lemon zaki ta Florida na kasar Amurka ya gabatar da cewa, tsarin kwastan na Turai ya nuna banbanci kan fitar da ruwan lemon da Amurka ta yi da dai sauransu.

A shekarar 1995, aka kafa kungiyar WTO, inda aka tsara wani tsarin warware takardamar cinikayya. Wani masani a fannin cinikayya, na sashen nazarin tattalin arzikin duniya na Peterson Chad Bown, ya nuna cewa, tsarin warware takadamar cinikayya ta WTO na da amfani kwarai, wanda ya hana kasar Amurka da ta dauki matakan na "rogue action" ko nuna karfin tuwo.

A cikin rahoton da kungiyar The South Centre ta fitar, an ce, bincike kan ayar 301 da Amurka ta gudanar, gami da tanadi mai lamba 232 da Amurka ta bullo da shi, game da buga haraji kan karafa da sanholo da aka shigo da su Amurka, sun baiwa hukumar ciniki ta duniya wato WTO mamaki sosai. Zargin da Amurka ta yiwa kasar Sin a cikin bincikenta kan ayar 301, zargi ne da aka yi bisa ma'aunin ita Amurka kanta, ba bisa ma'aunin WTO ba. Haka kuma a cikin abubuwan da Amurka ta zarga, akasarinsu ita Amurka da kungiyar OECD sun taba aikatawa, ko kuma suna ci gaba da aikatawa.

Game da zargin da Amurka ta yiwa gwamnatin kasar Sin game da manufofinta na goyon-bayan raya masana'antu da kimiyya da fasaha, rahoton da kungiyar The South Centre ta fitar ya ce, Amurka tamkar kasa ce dake rungumar cikakken 'yancin kan al'umma. Amma gaskiya ba haka ba ne. Shehun malami Robert Wade, na cibiyar nazarin harkokin bunkasuwa na kwalejin nazarin siyasa da tattalin arziki ta London ya ce, an hana tabo magana a kan wasu kalmomi a fagen siyasar Amurka, ciki har da "manufofin masana'antu" da "manufofin kimiyya da fasaha" da "manufofin yin kirkire-kirkire". Amurka ta dade tana ikirarin cewa, ita tana goyon-bayan kafa kasuwanni masu cikakken 'yanci, amma hakika dai, tun daga kafuwarta har zuwa yanzu, gwamnatin Amurka ta tsara wasu manufofin masana'antu da dama, wadanda suka wuce abun da ta fada.

Robert Wade ya ce, dalilin da ya sa kasar Amurka ta boye tallafin da ta bayar don raya fannin masana'antu shi ne, domin ra'ayin da kasar ta dauka na samar da wata kasuwa mai 'yanci. Idan an nuna ayyukan tallafin da ake bayarwa, to, wannan zai iya haddasa dakatar da ayyukan, da rufewar wasu masana'antu. Hakika tun daga shekarar 1791, an taba shawartar gwamnatin kasar Amurka da ta raya masana'antu, da nufin aza harsashi ga kokarin inganta aikin soja. Matakan da aka dauka a lokacin sun hada da karbar harajin kwastam, da ba da kudin alawus, da ware kudin gwamnati don sayen kaya, da gudanar da manyan ayyukan gini, da dai sauransu. An ce, shugabannin kasar Amurka da suka taba gabatar da matakan raya masana'antu suna da yawa.

Ga misali, bayan barkewar rikicin hada-hadar kudi a shekarar 2008, shugaba Obama ya taba bayar da tallafi ga fannin hada-hadar kudi, gami da wasu masana'antu.

Cikin rahotonta, Cibiyar The Kudu Center ta ruwaito wani jami'in kasar Amurka da ya halarci aikin raya kimiyya da fasaha na cewa, "Tabbas ne ana kallon wadannan ayyuka a matsayin matakan raya masana'antu, amma ba mu iya yin amfani da wannan kalma ba, don haka muna kiransa 'manufar nazari da kuma neman ci gaba'."

Ban da haka, rahoton ya ambaci nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin kare ikon mallakar ilimi. An ce kasar Sin ta ware makudan kudi don tallafawa kokarin kirkiro sabbin fasahohi. Yanzu kudin da kasar Sin ta zuba wa fannin nazarin kimiyya da fasaha ya kai kashi 20.8%, na daukacin kudin da ka zuba ma wannan fanni a duniya, wanda yawansa ya yi daidai da adadin kudin da dukkan kasashen dake nahiyar Turai suka ware don raya kimiyya da fasaha. Haka zalika, jaridar "Nikkei Asian Review" ta ba da labarin cewa, wajen yawan mallakar kira, jami'ar Tsinghua ta kasar Sin ta yi daidai da jami'ar MIT ta kasar Amurka. Saboda haka, a cikin rahoton Cibiyar, an ce kasar Amurka ta yi karya, bisa zargin kasar Sin da satar ilimi, da bayanai na kasar Amurka.

Manyan abokan ciniki na kasar Amurka, kamar su kungiyar EU da kasar Japan, dukkansu suna fuskantar matsalar sharadi na aya ta 301. Babban manazarci na cibiyar nazarin tattalin arzikin kasa da kasa ta Peterson, Chad Bown ya bayyana cewa, babban burin sharadin nan shi ne, gwamnatin kasar Amurka ta zama 'yar sanda, jimi'ar gabatar da kara a kotu, tawagar lauyoyi masu tallafawa gudanar shari'a da kuma alkali na duniya.

Manazarci na tattalin arziki John McMillan, ya taba kwatanta tsarin ciniki a tsakanin kasa da kasa da wani tsari na "idan ka taimake ni, ni ma zan taimake ka", amma a cewarsa, sharadin ayar 301 na kasar Amurka shi ne, "in ba ka taimake ni ba, zan shigar da kai cikin matsala".

Kasar Amurka ta yi binciken ayar 301 kan kasar Sin, domin gibin cinikayya dake tsakanin kasashen biyu, da kuma damuwarta kan babbar bunkasuwa da kasar Sin ta samu. Masanan tattalin arziki da dama sun taba bayyana cewa, kasar Amurka tana fama da gibin cinikayya, domin kankantar ajiyar kudinta, da kuma matsayin kudin kasar Amurka da aka adana tsakanin kasa da kasa. Da take ganin bunkasuwar kasar Sin cikin sauri, kasar Amurka ta fara nuna damuwa matuka.

Bisa rahoton da cibiyar "The South Center" ta fidda, an ce, ainihin dalilin da ya sa kasar Amurka ta gudanar da binciken ayar 301 kan kasar Sin, ba shi da nasaba da harkar ciniki, sai dai ya nuna burin kasar Amurka wajen hana kasar Sin samun bunkasuwar harkokin masana'antu, da kuma samun fasahohin da za su fi na kasar Amurka kyau.(Masu fassara:Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, Murtala Zhang, Maryam Yang, Bello Wang, dukkansu ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China