in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani Kan Wasan Hawan Dutse
2018-11-23 09:38:40 cri


Wasan hawan dutse ya shafi yadda ake hawan wani dutse, ko kuma wani dandalin da mutum ya gina, ko kuma sauka daga saman dutsen, ko dandalin. Sai dai saboda a kan gamu da hadari yayin da ake sauka daga saman dutse, don haka a kan kaucewa sauka ta hanyar da aka bi wajen hawan dutse, ganin yadda hanyar da ake bi wajen hawan wani dutse ta kan kasance wata mai wuya. Ban da haka kuma, wasan hawan dutsen da muke magana da kai a nan, shi ne wanda ke bukatar a dinga yin amfani da hannu don kama duwatsu, da daga jikin mutum sama, gami da kokarin kaucewa faduwa.

Game da gasanin da ake gudanar da su domin kwararun 'yan wasan hawan dutse, a kan sanya 'yan wasan su bi hanya daya, sa'an nan wanda ya kwashe mafi kankantar lokaci wajen isa sama ya ci nasara. Ko kuma a ba su wata hanya, inda bayan da aka fara hawa, wuyar da ake gamuwa da ita wajen hawa tana dada karuwa, sa'an nan wanda ya kai wani wurin da tsayinsa ya fi na saura ya zama zakara.

Wasan hawan dutse na bukatar karfin jiki da na zuciya, domin idan babu isashen karfin jiki, mutum zai iya gamuwa da matsala yayin da yake kokarin hawan dutse. Sa'an nan idan babu karfin zuciya, to, mutum zai iya jin tsoro, kuma watakila ba zai iya jure wahalar wasan, gami da isa kolin dutsen ba. Zai iya zama wani wasa mai tattare da hadari, idan mai hawan dutse bai san wasu kwararrun fasahohin hawan dutse ba, ko kuma bai san yadda za a yi amfani da kayayyakin kariya da yawa da ake bukata ba. Kasancewar wasannin hawan dutse iri daban daban ne a duniya, ta sa aka kasa wasan zuwa gidaje da dama.

Nau'ikan wasannin hawan dutse

Da farko, muna da "Free Climbing", ko kuma "fasahar hawan dutse cikin 'yanci" a Hausance. Wannan fasaha na bukatar a dogara kan karfin jiki wajen hawa wani dutse, yayin da sauran kayayyakin da ake amfani da su yayin hawa, su ne na ba da kariya ga mutum kawai, wato ba za a dogara kan kayayyakin da za su taimaka wajen sauwakawa jikin mutum hawa sama ba.

Sa'an nan akwai "Aid Climbing", wato hawa dutse da wasu na' urori na musamman. Wadannan na'urori, irinsu igiya, da kusa, ana dauke da su yayin da ake hawa. Za a dinga kafa kusa a kan dutse, a hada ta da wata igiya, wadda aka daure ta da jikin mutum. Sa'an nan za a dinga jan igiyar don daga jikin mutum. Za a maimaita wannan mataki don sanya mutum ya hau sama sannu a hankali. A kan dauki wannan fasaha ne lokacin da wani dutse ya zama mai wuya, ko kuma yana da hadari matuka ga fasahar hawan dutse cikin 'yanci, wato da hannu da kafa kawai.

Ban da wannan kuma, domin wadanda ba su dade wajen soma wasan hawan dutse ba tukuna, ko kuma wadanda ke son kyautata fasaharsu ta hawa, ana tsara wani irin wasan hawan dutsen da ake kira "Bouldering", wato hawa wani karamin dutse, ko kuma wani bango, wanda ba shi da tsayi. Rashin tsayi na rage damar gamuwa da hadari, saboda haka ba a yin amfani da igiya, gami da sauran na'urorin ba da kariya yayin da ake gudanar da wasan hawan dutse irin na Bouldering. Kawai za a shimfida wani abu mai taushi a kasa, da kuma sanya wani ya tsaya a gefe, ta yadda idan mutum ya fado, za a kare shi daga cin karo da wani abu mai tauri.

Muhallin gudanar da wasan hawan dutse

Bisa muhallin da ake gudanar da wasan hawan dutse a ciki, za a iya kasa wasan zuwa irin na "Indoor" da na "Outdoor", wato "ciki daki" ko kuma a "waje". Wasan hawan dutsen da ake gudanar da shi cikin daki, shi ne hawan da ake yi kan wani irin "bango" na musamman, wanda aka tsara shi tamkar wani bangare na dutse. Ban da haka, a jikin bangon, akwai wasu na'urorin da aka kafa domin mutum ya kama da hannu, ko kuma taka da kafa. Wannan bangon da aka kafa cikin daki ya ba mutane damar gwada fasahar hawan dutse a duk wani yanayin da ake ciki, ko ana ruwa, ko rana, akwai zafi, ko sanyi, dukkansu ba za su hana mutum shiga wasan hawan dutse ba, tun da muhallin hawan yana cikin daki. Masu koyon fasahar hawan dutse za su iya yin amfani da wannan irin bango na musamman don samun horo, yayin da sauran jama'a za su iya gwada fasahar hawan bangon don samun nishadi. Yanzu a kasar Sin a kan samu wannan irin bango da aka kafa cikin cibiyar kasuwanci, wato 'shopping mall', inda a kan ga yara da matasa suna kokarin hawan bangon domin nishadi.

Yayin da ake gudanar da wasan hawan dutse a waje, to, a kan gudanar da shi yayin da ake da hasken rana sosai. Domin wannan yanayi zai taimaka wajen rage santsi a kan dutse, da bai wa mutum sauki wajen hawa dutsen. Wani lokaci ma, idan wani mutum yana da cikakkiyar kwarewa wajen hawan dutse, wanda ya san fasahohin sarrafa na'urorin da ake bukata sosai, watakila zai gwada fasahar hawan dutse cikin dare, ko kuma a wani yanayi na ruwan sama, ko kuma iska, amma wannan gwajin da ake yi tabbas ne yana tare da dimbin hadurra.

Tarihin wasan hawan dutse

Wasu tsoffin zane-zanen da aka samu, sun nuna yadda Sinawa ke son fara hawan dutse a wasu shekaru 200 kafin haihuwar annabi Isa. Sa'an nan a nahiyar Amurka, mutanen da ake kiransu "Anasazi", wadanda suka zauna a kan duwatsu a karnin 12, su ma kwararru ne a fannin hawan dutse. Sa'an nan a kasashen Turai, wasu 'yan wasan hawan dutse suna amfani da wannan wasa don samun fasahohin da ake bukata wajen cimma matsayin koli na hawa wasu manyan duwatsu. Zuwa shekarun 1880, an fara mai da wasan a matsayin wani wasa mai zaman kansa, wato an raba shi daga cikin wasanni masu alaka da hawan manyan duwatsu. Ana ganin cewa, wasan hawan dutse na zamani, ya fara bullowa a nahiyar Turai, a karnin 19. Tsakanin shekarun 1920 zuwa 1960, hawan dutse da wasu na'urori na musamman irinsu igiya, da zoben jigo, ya fara farin jini. Wadannan na'urori da dabarun sarrafa, sun baiwa mutane damar hawan wasu manyan duwatsu wadanda a da ba a san yadda za a iya hawan su ba. Daga bisani, an ci gaba da kokarin kyautatawa, da inganta na'urorin da ake amfani da su wajen hawan dutse, yayin da ra'ayin mutane game da dabarun hawan dutse shi ma ya rika samun sauyi. Yanzu fasahar da ta fi samun karbuwa tsakanin masu hawan dutse ita ce "free climbing", wato hawa wani dutse ba tare da yin amfani da wata na'ura ba, ko kuma yin amfani da su domin ba da kariya ga mai hawa dutse kawai.

Salon hawan dutse

Ban da fasahohi daban daban da ake amfani da su wajen hawa dutse, yanzu salon da ake bi wajen hawan dutse shi ma ya bambanta bisa ra'ayi na daidaikun mutane. Cikin wani littafin da John Long, wani shahararren dan wasan hawan dutse, kuma marubuci na kasar Amurka, ya rubuta mai taken "Ta yaya za a hau wani dutse", ya ce, game da kwararrun 'yan wasan hawan dutse, isa kolin wani dutse kawai ba zai ishe su ba, kasancewar hanyar da ake bi wajen hawa wannan dutse ita ma na da muhimmacin gaske.

An kasa salon hawan dutse zuwa gidaje 3, wato na farko, "On sight", nufin kalmar shi ne "lokacin da aka ga wani abu". Ma'anar wannan salo ita ce, za a hau wani dutse kai tsaye ba tare da yin amfani da na'urori masu taimakawa hawa, ko kuma nazarin dabarun da aka taba dauka a baya ba. Yayin da salo na biyu shi ne wanda ake kira "Flashing", wannan salo ya yi kama da salon "on-sight" da muka ambata, kawai abin da ya sha bamban da na "on-sight" shi ne, salon "Flashing" na baiwa masu hawan dutse damar sanin hanyoyin da aka taba bi a baya wajen hawan dutsen, ta yadda zai iya zabar wanda a ganinsa ya fi dacewa. Ban da wannan kuma akwai salo na " Redpointing" , wanda shi salo ne na taka tsan-tsan. Masu bin salon " Redpointing" suna hawan wani dutse ne sau da yawa. Bayan an gwada wasu dabarun hawa da hanyoyin da ake bi kan wani dutse, to, zai sake hawa wannan dutse bisa wata dabarar da ta fi kyau.

Sauran fasahohi masu inganci game da wasan hawan dutse

Bayan da aka dade ana gwada hawan dutse, za a samu isasshiyar kwarewa don ci gaba da gwada wasu fasahohi masu inganci a fannin hawan dutse. Ga misali "Top rope", dabara ce da ake amfani da ita wajen hawan dutse, bisa yin amfani da zoben jigo. Da farko, za a kafa wani zoben jigo a saman dutsen, sa'an nan za a rataya wata igiya a kansa, wadda wani karshenta ke dauke da jikin mai hawa dutse, yayin da wani karshen igiyar na daban na hannun wani mutum da ke taimakawa mai hawan dutsen. Yayin da mai hawan dutse yake hawa, mataimakinsa zai rika jan igiyar sannu a hankali, don tabbatar da cewa wannan igiya za ta yi amfani, kasancewarta wata na'urar kariya ga wannan mutum dake hawa dutsen. Wato dai idan mutum ya fado, igiyar za ta hana shi sauka kasa ba kariya.

Ban da wannan kuma, akwai dabarar da ake kira "Lead", wadda ta fi hadari, idan an kwatanta da fasahar "Top rope" din. Wannan dabara ta "Lead" na nufin mutane 2 su hau dutse a lokaci guda. Daya daga cikin su shi ne wanda zai wuce gaba wato "lead" ko "jagora" da harshen Hausa. Shi wannan mutum mai ba da jagora zai fara hawa, yayin da igiyar da ke ba da kariya na hade da kusar da aka kafa kan dutse, sai dai ya kan wuce matsayin kusar, kafin ya kafa wata sabuwar kusa a sama. Sa'an nan mataimakinsa na dauke da igiya yana binsa. Bayan mai jagora ya hau wani matsayi, zai kafa wata kusa, ya rataya igiya a kai, sa'an nan zai ja mataimakinsa sama. Bayan da mataimakinsa shi ma ya hau matsayin, sai mai jagoran ya ci gaba da hawa. Idan ya fado, igiyar za ta hana shi sauka, duk da cewa, karfin saukarsa zai iya wuce wanda kusar da aka kafa za ta iya dauka. Idan hakan ya faru, dukkan mutanen biyu za su fuskanci babban hadari. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China