181024-sarkin-Kano
|
Mai martaba sarkin Kano a tarayyar Najeriya Muhammad Sunusi na II ya jagoranci wata babbar tawagar jami'an hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jahar Kano domin kawo ziyarar sada zumunta da kulla huldar cinikayya da wasu kamfanonin kasar Sin domin neman amincewarsu don su zuba jari a fannin raya masana'antun jahar Kano.
Tawagar ta ziyarci wasu biranen kasuwancin kasar Sin ciki har da Changsha da Jinan har ma da birnin Beijing, fadar mulkin kasar. Sashen Hausa na gidan radiyon kasar Sin CRI, ya samu zantawa da mai martaba sarkin, inda ya yi tsokaci game da makasudin ziyarar ta wannan karo.
Ga kalaman mai martaba sarki Muhammadu Sunusi na II dangane da wannan ziyarar.