in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron bitar bunakasa koyar da yaren sinanci a Najeriya
2018-10-21 16:41:41 cri
A jiya Asabar aka gudanar da taron bitar hanyoyin kyautata koyar da yaren sinanci wanda ya gudana a Abuja babban birnin Najeriya.

Bitar ta wuni guda zata taimaka wajen karfafa huldar raya al'adu tsakanin Najeriya da kasar Sin, kamar yadda cibiyar raya al'adun kasar Sin dake Abuja ta sanar da hakan.

Sinawa masu yawa da malamai 'yan asalin Najeriya dake koyar da yaren sinanci, musamman wadanda suka zo daga jami'ar nazarin al'adun kasar Sin ta Confucious dake Najeriya, da kwalejoji da makarantun firamare da sakandare daban daban daga sassan Najeriyar ne suka halarci taron.

Akwai kuma jami'ai daga ma'aikatar ilmi ta tarayyar Najeriya da suka halarci taron bitar.

Zhou Pingjian, jakadan kasar Sin a Najeriya, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a gefen taron bitar cewa, taron yana da matukar muhimmanci bisa la'akari da yadda ake kara samun cudanyar mu'amala tsakanin mutum da mutum na al'ummomin kasashen biyu wanda hakan muhimmin ginshiki ne na kara karfafa dangantaka tsakanin Sin da Najeriya.

A Najeriya, a halin yanzu ana karantar da yaren sinanci a makarantun Confucious biyu dake kasar, da kuma wasu kwalejoji da makarantun firaimare da sakandare masu yawa a kasar.

Nkiru Osisioma, mataimakin darakta a ma'aikatar ilimi ta tarayya, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, akwai bukatar a kara karfafawa makarantun ilmi a Najeriya gwiwa wajen koyar da darrusan yaren sinanci a matsayin wata hanya ta kara zurfafa dangantaka tsakanin Najeriya da kasar Sin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China