181022-Stefania-Bilkisu.m4a
|
A shekarar 1981, matashiyar kasar Italiya Stefania Stafutti 'yar shekaru 23 a duniya a lokaci, ta iso nan kasar Sin don biyan bukatunta na sha'awar wannan tsohuwar kasa dake gabashin duniya, da kaunar da take nuna wa al'adun kasar Sin. Tun daga lokacin, ta soma alakarta da kasar Sin har tsawon kusan shekaru 40. Ta shaida manyan sauye-sauyen da kasar Sin ta samu daga farkon lokacin da ta soma yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare har zuwa yanzu.
Kwanan baya, wakilinmu ya kai ziyarci Stefania Stafutti, babbar malama a kwalejin gabas na jami'ar Turin, kuma shugabar kwalejin Confucius na jami'ar a bangaren Italiya. To masu sauraro yanzu ga cikakken bayani game da hakan.