Gwamnan yankin Crimea ya bayar da sanarwa a kafofin watsa labaru na sada zumunta a wannan rana cewa, wanda ya kitsa lamarin wani dalibi ne dan aji hudu a kwalejin wanda tuni ya riga ya kashe kansa, an gano gawarsa a dakin karatu na kwalejin. Har yanzu dai ana ci gaba da bincike kan lamarin.
A wannan rana kuma, shugaban kasar Ukraine Petro Poroschenko ya gabatar da jawabi, inda ya zargi lamarin fashewar bom din da harbe-harben, a cewarsa wannan ne kisan gilla mai ban tsoro.
Kafin haka, kwamitin bincike na tarayyar Rasha ya yi aikin bincike kan lamarin bisa dokokin shari'a na kai farmakin ta'addanci, daga baya kuma ya sake gudanar da aikin bincike kan lamarin bisa dokokin shari'a na kisan gilla.
A watan Maris na shekarar 2014, an jefa kuri'ar raba gardama a yankunan Crimea da Sevastopol, masu jefa kuri'a sama da kashi 90 cikin 100 sun amince da ballewa daga Ukraine da komawa kasar Rasha. Amma, kasar Ukraine ba ta amince da hakan ba, tana adawa da ficewar yankunan biyu zuwa kasar Rasha. (Bilkisu)