in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na bayar da babbar gudummawa wajen yaki da wadanda suka aikata laifi tsakanin kasa da kasa
2018-10-16 13:50:53 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, Wang Qun, ya bayyana cewa, Sin muhimmiyar kasa ce dake bayar da gudummawa wajen yaki da mutanen da suka aikata laifuffuka tsakanin kasashe daban-daban, kana kuma tana son inganta hadin-gwiwa da sauran kasashen duniya domin tinkarar kalubalen dake tattare da laifuffukan da aka aikata tsakanin kasa da kasa, a wani kokari na raya makomar al'umma ta bai daya.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da babban taro karo na tara tsakanin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar yaki da miyagun laifuffukan da aka aikata tsakanin kasashe daban-daban ta MDD, Wang Qun ya ce, kamata ya yi kasashe daban-daban su sauke nauyin dake wuyansu bisa yarjejeniyar, da girmama dokoki gami da hakkin kowace kasa na yaki da miyagun laifuffukan da aka aikata, tare kuma da tabbatar da aiwatar da wannan yarjejeniya cikin adalci kuma ta hanyar da ta dace.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin na goyon-bayan kwararru masu yaki da miyagun laifuffukan da aka aikata ta kafar Intanet da su ci gaba da gudanar da ayyukan hadin-gwiwa a wannan fanni.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China