in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka  na shayar da duniya guba
2018-10-15 17:38:50 cri

A watan Yulin bana, Canada ta canja sunan ma'aikatar cinikayyar kasa da kasa ta kasar zuwa ma'aikatar cinikayyar kasa da kasa ta bai daya, makasudin sauyin shi ne,sa kaimi kan cinikayyar dake tsakanin kasar da sauran kasashen duniya, amma ba tsakaninta da kasar Amurka kawai ba, hakika tana son shiga kasuwar kasar Sin.

Amma, yarjejeniyar cinikayyar da sassan uku wato Amurka da Mexico da Canada suka daddale ba da dadewa ba wato USMCA, bai daidaita matsalar da Canada ke fuskanta ba, wato har yanzu tana dogara kan kasuwar Amurka sosai, haka kuma Canada ta rasa damar gudanar da cinikayya da sauran kasashen duniya.

Bisa babi na 32 na yarjejeniyar USMCA, an yi tanadin cewa, idan wata kasa ta daddale yarjejeniyar cinikayya maras shinge da wata kasa wadda ba ta aiwatar da manufar tattalin arzikin kasuwa ba, to sauran kasashen biyu suna iya ficewa daga yarjejeniyar sassan uku cikin watanni shida, ana ganin cewa, dalilin da ya sa aka rubuta wannan babi shi ne, hana gudanar da cinikayya da kasar Sin.

Jaridar "Financial Times" ta kasar Birtaniya ta buga wani sharhi cewa, hakika an rubuta babi da dama a cikin yarjejeniyar ne domin hana ci gaban kasar Sin, Amurka tana fatan kasashen Mexico da Canada su yi haka tare da ita.

Ministan kasuwancin Amurka Wilbur Ross yana mai cewa, babi na 32 na yarjejeniyar ya kasance kamar "wani maganin guba", yana sa ran za a rubuta irin wannan "babi na maganin guba" yayin da Amurka take daddale yarjejeniyar cinikayya maras shinge da sauran kasashen duniya, wadanda ke kunshe da Japan da kasashe mambobin EU da kuma Birtaniya wadda ta fice daga kungiyar. To, ko Amurka za ta cimma burin ware kasar Sin?

Da farko, yarjejeniyar ba ta nuna 'yancin kai da adalci ba, kasar Amurka ta kwashe 'yancin kasashen Canada da Mexico, sabo da karfinta a fannin ciniki.

Dangane da wannan sabuwar yarjejeniya, shugaban kungiyar kasuwanci ta kasar Canada Perrin Beatty ya bayyana cewa, ya kamata kasar Canada ta koyi darrasi a lokaci maras tsari, watau bai kamata kasar Canada ta ci gaba da dogaro kan wata kasuwar ciniki guda kadai ba. Ya kamata kasar ta habaka mu'amala da karin kasuwanni, domin magance wasu harkokin ciniki maras adalci.

Bisa matsin lambar da aka yi wa Canada, ministar harkokin wajen kasar Chrystia Freeland, ta bayyanawa takwaranta na kasar Sin Wang Yi cewa, Canada za ta ciyar da shawarwarin 'yancin ciniki dake tsakaninta da sauran kasashe gaba, tana fatan kasar Sin da sauran kasashen duniya za su tsaya tsayin daka kan tsarin cinikin dake tsakanin kasa da kasa, da kuma yaki da kariyar ciniki. Kuma, kasar Canada tana son karfafa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninta da kasar Sin, domin karfafa hadin gwiwar kasashen biyu bisa fannoni daban daban.

Ban da wannan kuma, ko sauran kasashe abokan cinikayyar Amurka za su yarda da sharadin da Amurka ta shata a wannan karo? Yanzu kasar Amurka ta riga ta fara matsawa kasar Japan lamba, inda ministan kasuwancin kasar Wilbur Ross ya ce, ya kamata Japan ta kaurar da masana'antu zuwa kasar Amurka, don rage rarar ciniki da ake samu a fannin cinikin motoci wadda yawanta ya kai dalar Amurka biliyan 40. A nasa bangare, Sonny Perdue, ministan aikin gona na kasar Amurka, ya bukaci kasar Japan da ta kara bude kofar kasuwarta a fannin amfanin gona. Ban da haka kuma, ya ambaci wani hakikanin batu, da kasar Japan ba ta amince da shi ba, wato "kasar Amurka ta dade tana ba Japan kariya". Mun san cewa, bayan yakin duniya na biyu, har zuwa yanzu, kullum kasar Amurka ta kan jibge sojojinta kimanin dubu 50 a kasar Japan. Yanzu kusan za a iya cewa kasar Amurka tana neman kasar Japan ta biya kudi bisa kariyar da aka ba ta.

Babu shakka, wadannan bukatun da kasar Amurka ta yi, sun kara manufa "mai guba" da kasar ta gabatar a wannan karo, za su sanya kasar Japan cikin hali mai wuya. Domin kasar Sin ita ce abokiyar ciniki mafi girma ta kasar Japan, kana kasar da ke karbar mafi yawan kayayyakin da kasar Japan take fitarwa. Wannan ya sa aka fahimci maganar da shugaban majalisar kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk ya fada, wato, idan ana da wani abokin da ake kiransa Amurka, ko za a kara bukatar wani abokin gaba?

Bayan Amurka ta tsaida kudurin janye jiki daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, a matsayin wani karfi mai muhimmanci da take kasancewa a duniya, kungiyar EU ta zabi kafa hukumar musamman tare da kasashen Rasha da Sin da nufin kaucewa kalubale daga wajen Amurka, da kuma ba da tabbaci wajen gudanar da cinikayya a tsakanin kasashen duniya da Iran yadda ya kamata.

Ana ganin cewa, ba zai yiwu EU ta ki yin la'akari da mulki da 'yancin kanta, ta sha wannan "maganin guba" na kasar Amurka ba, har ta sa hannu kan wannan yarjejeniyar maras adalci tare da Amurka. Kamar yadda shehun malama ta jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amurka Anne Kruger ta fada, "abin da ya fi muhimmanci shi ne, ala tilas gwamnatoci daban daban su tambaye kansu cewa, me ya sa za su yi shawarwari da kasar dake iya watsi da yarjejeniya a ko da yaushe?"

Na uku, yanzu tsarin karuwar tattalin arzikin kasar Sin na sauyawa, da nufin karfafa ingancin karuwar tattalin arziki ta hanyar kara matsayin sayen kayayyaki na al'ummar kasar. An kiyasta cewa, kasuwar sayen kayayyaki ta kasar Sin za ta kai matsayin na kasar Amurka, ko kuma za ta wuce matsayin na Amurka har ta kai na farko a duniya. A waje guda kuma, kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa abokiyar cinikayya ta farko ta kasashe da yankuna sama da 120 a duniya.

Ko shakka babu, babu wata kasa a duniya da ba ta so ta yi ciniki da kasar Sin. Alal misali, a kwanakin baya, kamfanin kera motoci na BMW na kasar Jamus ya sanar da cewa, zai ta zuba kudin EURO biliyan uku a kasar Sin, shi ma kamfanin mai na Exxon Mobil na Amurka ya daddale wata yarjejeniyar dala biliyan goma a kasar Sin. Haka zalika kamfanin kera motoci na Tesla na Amurka, zai bude wata hamshakiyar masana'anta a birnin Shanghai na kasar Sin. Dukkan wadannan al'amura sun nuna cewa, kasar da ba ta da zurfin tunani ce kadai ke ganin cewa za ta iya killace kasar Sin a fadin duniya.

Muna iya ganin cewa, duk da cewa kasar Canada da kasar Amurka sun kulla kawance tsakaninsu, amma Canadan na nuna himma da kwazo wajen gudanar da cinikayya tare da sauran kasashe baya ga Amurka, musamman kasar Sin.

Kasar Sin ta dade tana aiwatar da manufar hadin-gwiwa dake samar da moriyar juna, amma ita Amurka tana bin manufofin "sanya Amurka a sahun gaba" da kuma "wani bangare daya ne ke samun riba, ta yadda wani bangare na daban tilas ya yi hassara". Kila Amurka tana iya cin zarafin sauran wasu kasashe yayin da take gudanar da dangantakar diflomasiyya da su, amma sam ba za ta iya hana sauran kasashen duniya su yi cinikinsu ta hanyar da ta dace kuma bisa adalci ba. (Jamila Zhou, Maryam Yang, Bello Wang, Bilkisu Xin da Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China