in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Turkiyya da Saudiyya sun tattauna dangane da dan Jaridar Saudiyya da ya bata
2018-10-15 09:40:26 cri
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya tattauna ta wayar tarho da yammacin jiya, da Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiyya, game da batan Jamal Khashoggi, dan Jaridar kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu na Turkiyya, ya ruwaito wata majiya daga fadar shugaban kasar na cewa, yayin tattaunawar, shugabannin biyu sun jaddada muhimmancin kafa wani kwamitin hadin gwiwa da zai yi bincike game da lamarin.

Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya, ta wallafa a shafinta na Tweeter cewa, Sarki Salman ya kuma jaddada dangantaka mai karfi dake tsakanin kasarsa da Turkiyya, ya na mai cewa babu wanda zai iya yi mata illa.

Tun a ranar 2 ga watan nan na Octoba ne Jamal Khashoggi dan jarida mai kuma sharhi a jaridar The Washington Post, ya bata, tun bayan shigarsa ofishin Jakadancin Saudiyya dake Istanbul.

Wasu rahotanni da ba a tantance sahihancinsu ba, sun ce akwai yiwuwar an kashe Kashoggi a cikin ofishin jakadancin, abun da jami'an Saudiyyar suka musanta, suna masu bayyana shi da mara tushe. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China