181101-Bikin-baje-kolin-CIIE-na-farko-da-za-a-shirya-a-Shanghai-na-kasar-Sin.m4a
|
Daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamban shekarar 2018 ne za a bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar Sin(CIIE), inda za a shafe tsawon kwanaki shida ana gudanarwa a birnin Shanghai na kasar Sin.
Bikin zai hallara jami'an gwamnati da 'yan kasuwa da masu baje kolin kayayyaki da manyan masu sayayya daga sassa daban-daban na duniya. Haka kuma bikin baje kolin ya samarwa kasashe da yankuna sabbin hanyoyin kasuwanci da karfafa hadin gwiwa da bunkusa makomar harkokin cinikayya da tattali arzikin duniya.
Wannan shi ne karon farko da Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka ke halartar bikin baje kolin. Bayanai na nuna cewa, akwai sama da masu aikin sa kai 5,000 da za su ba da tallafi, yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na bana ko kuma CIIE a takaice, bikin da zai kasance irinsa na farko da kasar za ta karbi bakunci.
Mafi yawan masu aikin sa kan dai dalibai ne daga jami'oin Sin, da kuma sauran dalibai na manyan makarantun kasar. Ana kuma fatan za su ba da tallafi ga masu halartar baje kolin da harsunan turancin Ingilishi, da Japananci, da Rashanci, da Larabci da Sifaniyanci, da Portuguese da kuma Faransanci.
Masu shirya bikin sun ce masu aikin sa kan za su tallafawa masu halartar bikin baje kolin a fannin fassara, tun daga zuwansu har lokacin da za su koma kasashensu.
Kawo yanzu, sama da kasashe da yankuna 130 ne suka tabbatar da aniyarsu ta halartar wannan biki, wanda zai dada jaddada manufar kasar Sin ta gudanar da gyare gyare a cikin gida, da bude kofa ga kasashen waje, ta yadda sauran sassan duniya za su samu karin damammaki na shiga kasuwannin kasar. (Ahmed, Samisu, Ibrahim /Sanisu Chen)