181024-Zargin-da-mataimakin-shugaban-Amurka-ya-yiwa-kasar-Sin.m4a
|
A ran 4 ga watan Oktoban, mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya zargi manufofin gwamnatin kasar Sin da batun yankin Taiwan da ma tekun kudancin kasar ta Sin, lamarin da ka iya lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka. Sai dai kuma gwamnatin kasar Sin ta Allah wadai da kakkausar murya kan wannan jawabin,inda ta bayyana zargin na Pence da cewa ba shi da tushe ko kadan.
A yayin da mataimaki shugaban na Amurka ke zargin mahukuntan kasar Sin da tsoma baki a harkokin zabukan Amurkar sai ga shi kuma tsoffin sakatarorin harkokin wajen Amurka na cewa, ba su yarda da ra'ayin da Pence ya gabatar ba, misali Colin Powell da Madeleine Albright, sun bayyana cewa, kasar Sin ba abokiyar gabar kasar Amurka ba ce, bai kamata ba Amurka ta rika yin cacar baki da Sin.
Albright ta yi nuni da cewa, ko shakka babu kasar Sin babbar kasa ce wadda ke samun ci gaba cikin sauri, saboda dogon tarihin da take da shi da kuma kwazon da al'ummun kasar suke nunawa, kana Amurka ba ta yi abubuwan da suka dace a harkokin kasa da kasa yadda ya kamata ba, wannan ya sa kasar Sin ta samu karin damammaki na bunkasuwa.
Shi kuma tsohon sakatare Powell ya nuna cewa, ci gaban kasar Sin ya kawo moriya ga Amurka, kayayyakin da kasar Sin ke samarwa suna da inganci da kuma araha, haka kuma sun biya bukatun al'ummun kasar ta Amurka. Yanzu Amurka ta tada rikicin cinikayya da kasar Sin, rikicin da ya gurgunta moriyar masu sayayya na Amurka. Yana ganin cewa, gwamnatin Amurka ba ta dauki matakan da suka dace kan kasar Sin ba, ma'aikatar tsaron kasar ita ma tana mayar da kasashen Sin da Rasha da sauransu a matsayin abokan gaban ta, kan wannan, Powell yana ganin cewa, bai kamata ba Amurka ta yi haka, dole ne ta yi kokarin lalubo wata dabarar yin cudanya da sauran kasashen duniya, kuma wajibi ne Amurka ta yarda cewa, akwai bambanci tsakanin Amurka da sauran kasashen duniya.
Masu sharhi dai na ganin cewa, abubuwa marasa dacewa da Amurka ke dauka kan kasar Sin, ba za su kai ta ko'ina ba. Abu mafi muhimmanci shi ne, mutunta juna da warware bambance-bambancen dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa don amfanin bangarorin biyu. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)