181017-Shekaru-60-da-kafa-tashar-CCTV.m4a
|
A ranar 26 ga watan Satumban 2018 ne babban gidan talabijin na kasar Sin, wato CCTV ya shirya bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwa da ma fara sha'anin talibijin bayan kafa sabuwar kasar Sin, gidan Talabijin na CCTV wanda aka kafa shi a ran 1 ga watan Mayun shekarar 1958, a baya ake kira shi Talabijin na Beijing, tana da tashohi 50 da take watsa shirye-shirye daban-daban, inda sama da mutane biliyan guda ke kallonsa. CCTV Ya fara watsa shirye-shirye ne a ranar 2 ga watan Satumban shekarar 1958, kuma galibin wadannan shirye-shiryen sun kunshi labarai, shirye-shirye na musamman, da na ilimantarwa da ban dariya, da wasan kwaikwayo galibinsu na Opera.
Yanzu tashar CCTV tana daya daga cikin kafofin watsa labarai dake karkashin babbar hukumar kula da kafofin gidan Talabijin da Rediyo ta kasar Sin CMG.
Tashar ta koma watsa shirye-shirye ta tauraron dan-Adam na farko a 1972. Har zuwa shekarun 1970, tashar CCTV tana watsa shirye-shirye zuwa karfe sha biyu na dare. Sai dai a wasu lokutan ta kan watsa shirye-shirye da dare saboda dalibai.
Ya zuwa shekarar 1985, tashar CCTV ta kasance a sahun gaba wajen watsa shirye-shiryen talabijin a kasar Sin. A watan Yulin 2009, tashar ta kaddamar da tashar Larabci na kasa da kasa.
Yayin da tashar CCTV ke cika shekaru 60 da kafuwa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya nuna yabo sosai kan manyan nasarorin da aka cimma a fannin aikin talibijin na kasar, ya kuma ba da tabbaci kan bunkasuwa da nasarori da aka samu bayan kafuwar babbar hukumar gidan Gidan Rediyo da Talibijin ta kasar Sin wato CMG a takaice, kana ya bukaci da a bude sabon babi na aikin talibijin.
Shugaba Xi ya bukaci da a kafa sabuwar kafar watsa labaru da babu kamarta a duniya a fannin karfi na jagoranci, yada labaru da kuma tasiri.
A watan Maris na bana ne, aka kafa hukumar CMG, matakin da ya kai ga samar da dandamali mai kyau domin cimma wannan buri. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)