181010-Ranar-kafuwar-sabuwar-kasar-Sin-da-na-samun-yancin-kan-Najeriya.m4a
|
Ranar 1 ga watan Oktoban kowace shekara, rana ce da Sinawa ke murnar ranar da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949 ko kuma Jamhuriyar jama'ar kasar Sin.
A wannan rana ce Sinawa karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), suka ayyana nasarar 'yantar da kasar, bayan gwagwarmaya, inda aka saba shirya gagarumin biki a dandalin Tian'anmen dake birnin Beijing da ma sauran sassan kasar. Bikin da ke hallara shugabannin kasar da sauran jama'a daga bangarori daban daban na rayuwa.
Yayin wannan biki ne shugaban kasar Sin na wancan lokaci Mao Zedong, ya ayyana kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ko sabuwar kasar Sin, inda ya daga tutar kasar ta farko da kansa. Bayanai sun nuna cewa, sojoji da jama'a kusan 300,000 ne suka yi jerin gwano a yayin wannan biki.
Tun wannan lokaci ne kasar Sin take bunkasa a fannoni daban-daban, har zuwa yanzu da ta kasance kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Saboda muhimmancin wannan rana ne, ya sa gwamnatin kasar Sin ta kebe mako guda cur a matsayin ranakun hutu, inda 'yan kasar ke amfani da wannan lokaci don kai ziyara wuraren shakatawa tare da kai ziyara ga 'yan uwa da abokan arziki.
Bugu da kari, a wannan rana ce wato 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, ita ma Najeriya, babbar abokiyar kasar Sin a fannoni daban-daban, ta samu nata 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Burtaniya, inda nan ma ake shirya shagulgula don murnar wannan rana tare da bitar irin nasarorin da gwamnatocin wadannan kasashen suka samu ya zuwa wannan lokaci da kuma sassan da ke bukatar karin kulawa.(Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)