in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zargin Da Amurka Ta Yi Wa Kasar Sin Ya Nuna Damuwar Amurka
2018-10-05 21:09:48 cri

A yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a yammacin jiya Alhamis, mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence, ya zargi kasar Sin da tsoma baki cikin harkokin cikin gida da ma na zabukan Amurkar, Sannan ya kuma zargi kasar Sin game da manufofinta na cikin gida da na ketare. Dangane da wannan lamari, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, zargin da ya yiwa kasar Sin, ba shi tushe bare makama, kana kasar Sin ba ta yarda da wadancan kalamai ba ko kadan.

A hakika dai, kafin jawabin da Mike Pence ya yi, kasar Amurka ta taba fidda labarin cewa, gwamnatin kasar za ta gabatar da wata sabuwar manufa kan kasar Sin, lamarin da ya janyo hankulan kasa da kasa. Amma, wannan jawabin da Mike Pence ya yi ya sanyaya gwiwar kafofin watsa labarai kwarai da gaske, sabo da dukkansu zarge-zarge ne da Amurka ta taba yi wa kasar Sin a baya, kuma marasa tushe.

Amma me ya sa kasar Amurka ke son bata sunan kasar Sin a wannan lokaci? An lura cewa, ministan harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo zai kai ziyara a kasar Sin a ranar 8 ga wata, domin yin musayar ra'ayoyi da bangaren Sin kan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya wadanda suke jan hankulan bangarorin biyu. A daya bangaren, kasar Amurka tana tura jami'an kasarta zuwa kasar Sin domin yin shawarwari, dayan kuma, tana zargin kasar Sin a dukkan fannoni, wannan shi ne abin da ta saba yi. Sabo da cikin takaddamar cinikin da aka yi tsakanin kasar Sin da kasar Amurka cikin rabin shekarar da ta gabata, kasar Amurka ta kan yi amfani da wannan dabara ta "Yin fada domin neman yin shawarwari", ta yadda za ta samu karin moriyar tattalin arziki, sa'an nan, ta kara karfinta a fannin siyasa.

Cikin jawabinsa, Mike Pence ya yi wa kasar Sin suka mai tsanani, amma hakika dalilin da ya sa ya yi haka shi ne, maganar siyasa ta cikin gidan kasar da ayyuka masu alaka da zabe. Zancensa ya nuna yadda yake damuwa, da kokarin neman wani wanda zai iya dorawa laifi, kafin a fara yakin neman zabe. Kamar yadda wasu kafofin watsa labaru na kasar Amurka, da wasu masu nazarin al'amuran siyasa da kuma wasu jama'ar kasar suka bayyana, gwamnatin kasar Amurka na son janyo hankulan jama'a daga aikin binciken batun "hulda da kasar Rasha cikin sirri" da ake zargin shugaba Donald Trump da aikatawa, haka kuma tana neman samun karin kuri'u daga jama'ar kasar, bisa matakan nuna karfi da ake dauka kan kasar Sin. Har ila yau, tana neman kara matsawa kasar Sin lambo domin ta ba da kai bori ya hau.

Sai dai a hakika, kasar Sin ba ta so, kuma ba ta da lokacin tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe. Mu san cewa, da farko, kasar Sin kullum tana tsayawa kan manufar kin tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe. Sa'an nan na biyu, mutane fiye da miliyan 30 daga cikin al'ummar kasar na fama da talauci, don haka kasar tana shan aikin kula da wadannan mutane, da aiwatar da sauran shirye-shiryen raya kasa. Saboda haka sam ba za ta samu damar tsoma baki cikin harkokin sauran kasashe ba. Kan wannan batu ne ma har ministan kula da tsaron kasa na Amurka, Kirstjen Nielse ya furta a kwanakin baya cewa, "yanzu babu shaidu da za su tabbatar da cewa, kasar Sin na neman yin zagon kasa ga zaben majalisun kasar Amurka na shekarar 2018, ko kuma tana neman sauya sakamakon zaben." Ban da haka kuma, wasu kafofin watsa labaru na kasar Amurka da na sauran kasashe, irinsu CNN, da Reuters, dukkansu sun ce zargin da kasar Amurka ta yi a wannan karo ba shi tushe. Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin shi ma ya yi tambayar cewa, "wace kasa ce kan keta 'yancin kan sauran kasashe, da tsoma baki cikin harkokinsu na gida, gami da lahanta moriyarsu? Kasashe daban daban na duniya sun san amsar wannan tambaya."

Sinawa suna tsayawa kan al'adarsu ta "Kar a aikata laifi don samun moriya, kuma kar a ba da kai sakamakon tsoron matsin lamba". Haka zalika, suna mai da hankali sosai kan moriyar jama'a. Mun san cewa huldar dake tsakanin Sin da Amurka tana da matukar muhimmanci, wadda kuma ke da tasiri kan moriyar kasashen biyu, gami da burin duniya na neman zaman lafiya da ci gaba. A kwanakin nan, gwamnatin kasar Sin ta sanar da wata takardar bayani mai taken "batun gaskiya dangane da takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka, da ra'ayin kasar Sin", inda aka yi amfani da alkaluma da dama, da misalan hakikanan abubuwan da suka faru, don shaida huldar hadin kai dake tabbatar da moriyar juna da ake samu tsakanin kasashen Sin da Amurka, tare da nuna cewa "yin hadin gwiwa zai fi samar da alfanu ga Sin da Amurka, gami da duk duniya."

Ya kamata a gane cewa, ko da yake a kan tayar da rikice-rikicen cinikayya tsakanin kasar Sin da ta Amurka bayan Donald Trump ya hau kan mukamin shugaban gwamnatin kasar, adadin cinikayyar da aka yi tsakanin kasashen biyu a shekarar 2017 ya kai dalar Amurka biliyan 583.7, wato ya ninka har sau 233 idan aka kwatanta shi da na shekarar 1979, wato shekarar da aka kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. A waje daya, kasashen Sin da Amurka, dukkansu zaunannun membobi ne na kwamitin sulhun MDD, suna da dimbin damammakin yin hadin gwiwa a fannonin yakar ta'addanci, tsaron shafukan intanet da sararin samaniya da shawo kan yake-yake da sauran batutuwan da suke shafar duniya baki daya. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, a cikin shekaru kusan 40 da suka gabata bayan kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakaninsu, tushen sada zumunci tsakanin al'ummomin kasashen biyu ya samu karfafuwa sosai. Wadannan abubuwa su ne ke ba da tabbaci ga kokarin tabbatar da ganin an raya dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka kamar yadda ya kamata.

A 'yan kwanakin baya, a lokacin da tsohon direkta mai kula da harkokin Asiya a kwamitin kwantar da kura na kasar Amurka, kuma mai fashin baki a cibiyar nazari ta Brookings ta kasar, Mr. Jeffrey Bader yake ganawa da manema labaru, ya yi amfani da wani rahoton sa ido kan dangantakar dake tsakanin kasashen Amurka da Sin da cibiyar ta fitar a kwanan baya, inda ya ja kunnen gwamnatin Donald Trump, cewa idan gwamnatinsa ta nuna taurin kai, ta yi watsi da yin mu'amala da bangaren Sin, hakan zai kawo illa ga Amurka. Sannan Henry Alfred Kissinger, tsohon sakatare mai kula da harkokin wajen kasar Amurka, shi ma ya gargadi shugabannin Amurkar, inda ya ce, ya kamata su san ainihin moriyar kasar. Sannan kada su yi kuskure wajen yin la'akari da batutuwan dake shafar kasar Sin sakamakon wasu rikice-rikicen dake kasancewa a yanzu tsakanin kasashen biyu.

Ko da yake gwamnatin kasar Amurka ta kan canja manufofinta kan kasar Sin, amma manufofin da kasar Sin take dauka kan kasar Amurka na kasancewa a fili ba tare da tangarda ba, wato rashin tashin hankali balle yakar juna, sannan mutunta juna da yin hadin gwiwa domin neman moriya tare. Farfesa Henry Kissinger ya taba ba shugaba Donald Trump shawarar cewa, ya shigar da wanda ya san tarihi da al'adun kasar Sin cikin gwamnatinsa, ta yadda zai iya zama mai shiga tsakani tsakanin gwamnatocin Amurka da Sin. Amma bisa kalaman da Mike Pence ya bayar, an gane cewa, har yanzu babu irin wannan jami'i a cikin gwmnatin kasar Amurka mai ci. Ya zama wajibi ga gwamnatin Amurka mai ci ta saurari shawarar da wannan shehun malami ya bayar. Idan kasar Amurka, wadda har yanzu ita ce kasa mafi karfi a duk duniya, ta soma saurara da fahimta da kuma mutunta ra'ayoyin sauran kasashen duniya, za ta iya cimma burinta na sake zama wata "kasaitacciyar" kasa. (Sanusi Chen, Bello Wang, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China