in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kokarin Samar Da Kyakkyawar Makoma Ga Daukacin Bil-Adama
2018-10-05 20:49:01 cri

A yayin babban taron MDD na baya-bayan nan babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su yi kokarin hada kai don samo hanyoyin magance matsalolin da duniya ke fuskanta. Wannan kira ya yi dai-dai da taken babban taron majalisar na wannan shekara "shugabancin duniya da daukar nauyi tare wajen samar da zaman lafiya, daidaito da al'umma mai dorewa" Amma sabanin haka, shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da damar da yake jawabi a babban taron na MDD wajen gabatar da manufar kasarsa da farko. Yana mai cewa, Amurka ta zabi kasance saniyar ware maimakon kasancewa da sauran kasashen duniya, matsayin da ya gamu da suka daga galibin shugabannin kasashen duniya, ciki har da wasu tsoffin kawayen kasar ta Amurka.

A 'yan shekarun nan wasu kasashen da suka ci gaba sun kara karkata ga tsarin zaman 'yan marina, lamarin dake haifar da kalubale ga hadin gwiwar kasa da kasa da tsarin tafiyar da harkokin duniya. Wannan shi ne dalilin manufar kasar Sin na goyon bayan tsarin kasancewar bangarori ya samu goyon baya daga al'ummomin kasa da kasa. A wata hirar da ya yi da gidan rediyon kasar Sin CRI yau shekaru biyu da suka gabata, wani masani dan kasar Amurka Robert Kuhn, ya yaba shawarar nan ta "Ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinpjng na kasar Sin ya gabatar a shekarar 2013. Yana mai cewa, ta ba da muhimmiyar gudummawa ga ci gaban duniya baki daya.

Shi ma ministan harkokin wajen kasar Hungry Peter Szijjarto, ya ce shawarar ta samar da wata sabuwar odar duniya, saboda a baya jari na kai koma ne kawai daga kasashen yamma zuwa gabas domin neman kwadago mai araha, amma yanzu karin jari gami da fasahohi na zamani masu inganci daga kasar Sin na kara shiga kasashen yamma. Don haka ya yi na'am kan yadda kasar Sin take zuba jari a bangaren muhimman kayayyakin rayuwar jama'a a kasarsa, da ma yadda hakan suke hade sauran kasashe makwabta wadanda suke taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki a yankin.

Ita kuma Michele Geraci, mataimakiyar sakatare mai kula da ci gaban tattalin arziki a sabuwar gwamnatin Italiya, ita ce take jagorantar shirin nan mai suna " Task Force China" a wani mataki na zakulo damammaki na hadin gwiwa da kasar Sin, musamman a fannin ayyukan da suka shafi shawarar "ziri daya da hanya daya" da ma a Afirka.

Tun lokacin da aka kaddamar da shawarar shekaru biyar da suka gabata, shawarar "ziri daya da hanya daya", ta samar da kyakkyawan sakamako ga kasashen dake cikinta musamman a fannin tattalin arziki. Manyan cibiyoyi na kasar Amurka, kamar cibiyar hada-hadar hannayen jari ta Brookings, ta wallafa wani rahoto a watan Satumban wannan shekara, inda ta nuna cewa, ayyukan raya kasa da kasar Sin ta gudanar suna taimakawa wajen samar da ci gaba mai dorewa. Cibiyar ta kuma nazarci tasirin wasu ayyuka ci gaba guda 4,300 da kasar Sin ta gudanar a kasashe 138, kuma binciken ya nuna cewa, wadannan ayyuka sun taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin wadannan kasashe. A takaice, taimakon da kasar Sin ta baiwa hukumomin wadannan kasashe ya samar da karuwar kaso 0.4 cikin 100 na ci gaban tattalin arzikin kasashen na shekaru biyu bayan samar da wadannan kudade.

Kaza lika rahoton ya bayyana cewa, duk da cewa da yawa daga hukumomin bada tallafi, da bankunan samar da ci gaba, na ikirarin maida hankali wajen samar da ci gaba daga dukkanin fannoni, a zahiri hakan bai samar da sauyin da ake fata ba. Sin, a nata bangare, ta kaddamar da shirye shiryen bunkasa tattalin arziki, wadanda aka tanada musamman domin yankunan karkara, da wuraren dake lunguna masu tattare da mutane dake da kananan samun kudin shiga, da masu matsakaicin samun kudaden shiga, wadanda ke da tarihi na shan wahalhalu daga watsi da aka yi da su, ko nuna masu wariya.

Har wa yau, kasar ta kuma samar da nata tsari, na hade sassan da suka ci gaba, da wadanda ke a kebe, da ma wadanda ke bakin ruwa masu ci gaba, domin rage gibin ci gaba tsakanin sassan kasar.

Tashar jiragen ruwa ta Piraeus Port, tasha mafi girma a kasar Girka, kuma mafi girma a yankin tekun Meditereniya, muhimmin aiki ne tsakanin Sin da Girka karkashin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya.

La'akari da nasarar shawarar ziri daya hanya daya, Amurka, da kungiyar tarayyar Turai, da ma wasu kasashe masu wadata, na shirin samar da nasu salon wannan shawara domin hade yankinsu. Sau da yawa a kan yi hasashen haka a matsayin wani yunkuri, na kalubalantar tasirin da Sin ke yi a harkokin kasa da kasa. Sai dai duk da haka, Sin na maraba da wannan lamari, musamman duba da yadda matakin ke nuna muhimmancin yin hadin gwiwa wajen bunkasa tattalin arzikin kasashe, tare da gina duniya dake bude kofofinta na tattalin arzikin ga kowa.

Shekaru biyu da suka gabata a birnin Hangzhou, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana aniyar Sin na bude kofa ga duniya, a matsayin wani abu da Sin ta kirkira ga duniya. Kasar Sin ba ta samar da shi domin kafa wani salo na karfafa tasiri ba. Maimakon haka, mataki ne dake samar da fa'ida ta ci gaba a dukkanin sassan duniya.

Shekaru 40 bayan da Deng Xiaoping ya kaddamar da manufar Sin ta bude kofa ga sassan duniya, da aiwatar da sauye sauye, kasar ta kara azama wajen binciko sabbin hanyoyi, wadanda za su baiwa kasashen duniya baki daya damar aiki tare, domin cimma moriyar juna da ake fata. (Ibrahim Yaya, Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China