Jiya Litinin, rana ce da MDD ta kebe domin lura da batun muhallin zaman al'umma. Albarkacin wannan rana ta musamman, shirin MDD mai kula da muhallin zaman al'umma (UN-Habitat), ya shirya wani biki, na ba da kyautar karramawa a hedkwatarsa dake Nairobin kasar Kenya.
A wajen bikin, birnin Xuzhou na kasar Sin, ya samu kyautar yabo, bisa ci gaban da ya samu a fannin sauya tsare-tsaren birnin, tare da neman ci gaban tattalin arzikinsa.
Da take tsokaci a yayin bikin, shugabar shirin UN-Habitat Maimunah Mohd Sharif, ta ce ya kamata a yada fasahohin ci gaba, da kasar Sin da sauran wasu kasashe suka samu, a fannin kula da muhallin zaman al'umma, musamman ma ga kasashen dake kan hanyar tasowa, wadanda suke fuskantar dimbin kalubaloli a wannan fanni. (Bello Wang)