in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gudummawar Peng Liyuan na yaki da tarin fuka da cutar kanjamau a duniya
2018-10-04 15:10:01 cri

Cutar tarin fuka da kanjamau ko Sida, na daga cikin cututtukan dake halaka miliyoyin jama'a a duniya. Wannan ya sa gwamnatocin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da masu zaman kansu da masana da masu ba da agaji gami da ma'aikatan sa-kai ke kokarin ganin bayan wadannan cututtuka. Haka su ma matan shugabannin kasashe ba a bar su a baya ba a wannan fafutuka.

Madan Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, na daga cikin matan dake ba da gudummawa wajen yaki da cutar tarin fuka da kanjamau. Wannan ya sa MDD ta nada ta a matsayin jakadiyar yaki da cutar tarin fuka da kanjamau .

Sakamakon najimin kokarin da take yi, ya sa ta zama jakadiyar yaki da cutar tarin fuka da kanjamau ta kasar Sin a shekarar 2007, kana jakadiyar fatan alheri a shekarar 2011. Wannan wani babban nauyi ne da kullum take kokarin ganin na sauke.

A jawabin da ta gabatar yayin babban taron MDD karo na 73 na wannan shekara, uwar gida Peng Liyuan ta bayyana cewa, yau kusan sama da shekaru 10, a kowace ranar 24 ga watan Maris din kowa ce shekara, ta kan ziyarci al'ummomin dake fama da cutar tarin fuka, domin ta ilimantar da su, yadda za su canja halayensu da kara daukar matakan magance wannan cuta. A wannan shekara ta ziyarci lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin, inda ta sanar da matasa dalibai wasu muhimman bayanai game da cutar tarin fuka da yadda za su zauna cikin koshin lafiya, sannan na sanar da su muhimmacin yin tsafta.

Madan Peng Liyuan ta yi amfani da wannan dama wajen godewa kafofin watsa labarai da masu ba da goyon baya gami da masu aikin sa-kai dubu 700 a shirye-shiryen yaki da cutar tarin fuka a kasar Sin, Sai dai duk da tarin nasarorin da aka samu wajen yakar wannan cuta, Peng Liyuan ta ce matsalar isassun kudade da hanyoyin magance cutar, na daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta a duniya. Hukumar lafiya ta duniya WHO ta riga ta kaddamar da matakan yaki da cutar tarin fuka, don haka lokaci ya yi da za a dauki matakan da suka dace.

Daga karshe ta yi kira ga kowa da kowa da ya shiga a dama da shi a kokarin da ake na inganta rayuwar miliyoyin jama'a dake fama da cutar tarin fuka da ma kawo karshen cutar baki daya a duniya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim / Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China