in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana matsayinta kan takaddmar cinikayyar dake tsakaninta da Amurka
2018-09-27 08:32:23 cri

A ranar Litinin gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da shaidu da matsayinta kan takaddamar cinikayya dake tsakaninta da kasar Amurka, inda ta yi bayani filla-filla kan hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fannin tattalin arziki da cinikayyar moriyar juna, sannan ta karyata zargi maras tushen da Amurka ta yiwa kasar Sin a cikin rahoton bincikenta mai lamba 301, tare kuma da bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin dangane da takaddamar cinikayyar dake tsakaninta da Amurka.

Takardar bayanin ta kunshi haruffan Sinanci 36000,da kuma sassa guda shida(6)ta kuma zayyana dimbin alkaluma da misalai da sauransu, wadanda akasarinsu aka tsamo su daga hukumomin gwamnatin Amurka da manyan kamfanonin kasashen duniya da shahararrun cibiyoyin nazarin kasa da kasa gami da littattafan da shahararrun masana suka rubuta.

Haka kuma takardar bayanin, ta nuna damuwa gami da ra'ayoyin gwamnatin kasar Sin kan takaddamar cinikayya dake tsakaninta da Amurka, da kuma namijin kokarin da Sin take yi wajen kiyaye moriyar bai daya ta Sin da Amurka gami da tsarin cinikayya na fadin duniya.

Na farko takadar bayanin, ta bayyana hakikanin shaidu da gaskiyar lamari kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, da bayyana ra'ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da ra'ayin nuna fin karfi da Amurka ke nunawa, gami da illolinsu.

Daya daga cikin hujjojin da Amurka ke fakewa da su wajen kaddamar da takaddamar cinikayya kan kasar Sin shi ne, wai kasar Sin ta fi Amurka cin moriya daga hadin-gwiwarta da Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya, saboda haka, Amurka ta bukaci da a gudanar da cinikayya "cikin adalci" da budewa juna kofa "daidai wa daida". Kalaman na kasar Amurka suna iya kawo rashin fahimta ga mutanen da ba su san hakikanin gaskiyar al'amarin ba. Don haka, kalaman Amurka na cewa wai ta yi hasara, sam ba su da tushe balle makama. Har wa yau kuma, takardar bayanin ta gabatar da kwararan shaidu da dama don karyata wasu zarge-zargen da Amurka ta yiwa kasar Sin, ciki har da rashin daidaito tsakanin cinikayyar Sin da Amurka, da rashin adalci tsakanin cinikayyarsu, da satar 'yancin mallakar fasaha, da tilasta a yi musanyar

Takardar bayanin ta bayyana matsayin kasar Sin kan batun tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da Amurka da kuma alakar dake tsakanin kasa da kasa da hanyar da ta dace wajen warware takaddamar cinikayya a tsakanin Sin da Amurka.

Takardar bayanin na ganin cewa, matsayin ci gaba da ma tsarin tattalin arzikin kasashen biyu ya bambanta, don haka, ba wani abu ba ne idan aka samu takaddamar cinikayya daga lokaci zuwa lokaci. Amma, abu mai muhimmanci shi ne, yadda kasashen biyu za su karfafa amincewa da juna, da bunkasa alakarsu da ma yadda za su warware bambance-bambancen dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Masu fashin baki na cewa, takaddamar cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka na iya yin tasiri ga zaman lafiya da wadatuwar tattalin arzikin duniya, ya kamata a warware matsalar yadda ya kamata. Domin ko da yaushe kofar kasar Sin a bude take wajen yin shawarwari, amma dole ne a yi shawarwari bisa tushe na girmama juna, daidai wa daida, da kuma cika alkawari, domin babu wanda zai yi nasara a yakin cinikayya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanisu Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China