180921-bikin-tsakiyar-yanayin-kaka-na-sinawa-lubabatu.m4a
|
Bikin Zhongqiu na daya daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na Sinawa, wanda a kan yi shi a ranar 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato ya fado a daidai tsakiyar yanayin kaka, shi ya sa ake kiransa bikin Zhongqiu, ma'ana wato bikin tsakiyar yanayin kaka. Kuma a wannan shekara, ya fado daidai a ranar 24 ga watan Satumba. A biyo mu cikin shirin, domin jin karin haske. (Lubabatu)