in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yang ya taya Ningxia murnar cika shekaru 60 da kafuwa
2018-09-21 10:41:09 cri
Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin Wang Yang, ya taya jihar Ningxia na kabilar Hui mai cin gashin kansa murnar tarin nasarorin da ma ci gaban da ya samu cikin shekaru 60 da suka gabata.

Jami'in ya bayyana hakan ne yayin da yake yiwa wani taron jama'a jawabi a Yinchuan, babban birnin Ningxia dangane da bikin cika shekaru 60 da kafa yankin.

Wang, mamba zaunannen kwamitin hukumar siyasa na kwamitin koli na JKS, kana shugaban hukumar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin(CPPCC) shi ya jagoranci tawagar da ta halarci bikin cikar yankin 60 da kafuwa.

Ya ce, a cikin shekaru 60 din da suka gabata jihar Ningxia, karkashin jagorancin kwamitin koli na JKS ya samu gagarumar ci gaba a fannin tattalin arziki, da inganta rayuwar al'umma da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Don haka ya yi kira da a kara daukar matakan inganta tattalin arziki, da hadin kan kabilu da kare muhalli da rayuwa mai inganci tsakanin al'ummun jihar, ta yadda jihar ya Ningxia za ta shiga cikin rukunin al'umma mai matsakaicin kudin shiga kamar sauran takwarointa dake kasar.

Mataimakiyar firaministan kasar Sin Sun Chunlan ta gabatar da sakon taya murna a madadin kwamitin koli na JKS da kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar da majalisar CPPCC da hukumar kula da harkokin sojojin kasar.

Alkaluma na nuna cewa, ma'aunin GDPn yankin ya karu daga Yuan miliyan 328 a shekarar 1958 zuwa sama da Yuan biliyan 345 a shekarar da ta gabata. An kuma samu nasarar rage matsayin talauci daga sama da kaso 70 cikin 100 zuwa kaso 6 cikin 100.

Kimanin mutane 21,000 daga sassan rayuwa daban-daban da suka wakilci dukkan kungiyoyin kabilun Ningxia ne suka hakarci bikin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China