in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin tattaunawa karo na 2 kan hanyar siliki ta teku ta karnin 21
2018-09-20 14:48:55 cri

A jiya Laraba da maraice ne, aka bude taron dandalin tattaunawa karo na 2 kan hanyar siliki ta teku na karnin 21 a birnin Zhuhai na kasar Sin, wanda babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG da gwamnatin lardin Guangdong suka karbi bakuncin gudanar da shi. Taken taron tattaunawar shi ne "sabuwar hanyar siliki ta teku a sabon zamanin da ake ciki", manufar taron ita ce gadan tunanin tarihi da shigar da sabon tunani a sabon zamanin da ake ciki.

A shekaru 5 da suka gabata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar raya hanyar siliki ta teku cikin karni na 21, wadda ta shigar da sabon tunani kan tsohuwar hanyar siliki ta teku a tarihi. A cikin wadannan shekaru 5 da suka wuce, yawan cinikin kayayyakin dake tsakanin Sin da kasashen da hanyar ta ratsa ya kai fiye da dala biliyan dubu 5, kuma yawan jarin da kasar Sin ta zuba ga kasashen kai tsaye ya kai fiye da dala biliyan 60, kana an kafa yankunan hadin gwiwa na tattalin arziki da cinikayya a kasashe fiye da 80 da hanyar ta ratsa, wadanda suka samar da ayyukan yi da dama, kuma hakan ya amfanawa jama'ar dake yankunan. Lardin Guangdong wuri ne da aka fara aiwatar manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, kana muhimmin yanki ne na raya hanyar siliki ta teku. Gwamnan lardin Guangdong Ma Xingrui ya yi jawabi cewa,

"A shekaru 5 da suka gabata, gwamnatin lardin Guangdong ce ta fara samar da shirin shiga aikin aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya' a kasar Sin bisa bukatun kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta Sin, wanda ya taimaka ga yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen da hanyar ta ratsa. Lardin ya hada gwiwar kasashen a fannonin tsara manufofi da gina ayyukan more rayuwa da saukaka harkokin ciniki da zuba jari da kuma cudanyar jama'arsu. Muna imani da cewa, bisa ga taron dandalin, bangarori daban daban za su kara yin mu'amala da juna, ta yadda za su cimma daidaito kan fadada hadin gwiwarsu."

A yayin bikin bude taron, shugaban sashen fadakar da jama'a na lardin Guangdong Fu Hua ya gabatar da rahoton aikin kamfanonin lardin Guangdong na raya shawarar " ziri daya da hanya daya", inda aka shaida nasarorin da kamfanonin lardin Guangdong suka samu a fannonin amsa kiran shawarar "ziri daya da hanya daya", da kokarin yin hadin gwiwar samun moriyar juna a tsakanin kasashe da yankuna dake cikin shawarar "ziri daya da hanya daya". Fu Hua ya bayyana cewa,

"Za mu yi amfani da damar gabatar da rahoton, da ci gaba da yin kokari wajen yin shawarwari da more fasahohi da hadin gwiwar samun moriyar juna da mu'amala da juna yadda ya kamata, da ci gaba da taimakawa kamfanonin lardin Guangdong su shiga aikin raya 'ziri daya da hanya daya' don ba da gudummawa ga samun bunkasuwa mai dorewa a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasashe da yankunan dake cikin shawarar 'ziri daya da hanya daya'."

A yayin da aka bunkasa hanyar siliki ta teku a tarihi, kasar Sin ta yi ciniki tare da kasashe fiye da 60 da hanyar siliki ta teku ta ratsa, wannan ya shaida yanayi mai kyau na yin ciniki a tsakanin Sin da kasashen duniya da dama. Farfesa Stefania mai nazari a kan harshen Sinanci a jami'ar Turin ta kasar Italiya, ta bayyana a gun bikin bude taron cewa,

"Ana iya yin jigilar durian daga kudu maso gabashin Asiya zuwa kasar Sin, kana ana iya yin jigilar 'ya'yan itatuwan nan da ake kira Litchi daga lardin Guangdong na kasar Sin zuwa birnin Rome na kasar Italiya, kuma hakan ya faru ne a sakamakon yadda aka saukaka harkokin yin ciniki da juna bisa shawarar 'ziri daya da hanya daya'. Shawarar 'ziri daya da hanya daya' muhimmin sha'ani, kuma sha'ani ne da za a dade ana gudanar da shi, wadda ta kasance tamkar wata gada a tsakanin kasashen duniya, babu shakka dukkan kasashe masu son zaman lafiya da neman samun bunkasuwa da jama'arsu za su goyi bayan shawarar."

Shugaban babban rukunin CMG Shen Haixiong ya bayyana a gun bikin bude taron cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 40 da aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, kana shekara ce ta cika shekaru 5 da shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya". Taron tattaunawar na wannan karo zai shaida sabbin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da shawarar raya hanyar siliki ta teku cikin kanin 21, da kuma aikin yin mu'amala da juna a fannin al'adu. Babban rukunin CMG zai ci gaba da watsa da ra'ayoyin Sin, da kiyaye tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban da watsa labaru game da tunanin al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China