in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kusan yara da matasa miliyan 303 ne ba sa zuwa makaranta a duniya
2018-09-20 09:51:54 cri
Rahoton asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya ce kusan yara da matasa miliyan 303, dake tsakanin shekara 5 zuwa 17 ne ba sa zuwa makaranata a duniya.

Rahoton da ya yi nazari kan makomar yaran da ba sa zuwa makaranta, ya ce 1 bisa 3n adadin, wato kusan miliyan 104 na yaran, na kasashen dake fama da rikici ko iftila'i.

Ya kara da cewa, 1 cikin yara 5 'yan shekara 15 zuwa 17 a kasashen da ke fama da rikici, ba su taba shiga aji ba, sannan 2 cikin yara 5 ba su kammala makarantar firamare ba.

Har ila yau, rahoton ya ce bisa halin da ake ciki yanzu, adadin yara 'yan shekara 10 zuwa 19 zai karu zuwa biliyan 1.3 ya zuwa 2030, wanda zai karu da kaso 8. Inda ya ce samarwa manyan goben ingantaccen ilimi da damarmakin aiki mai kyau, zai haifar da dimbin alfanu ga tattalin arziki da zaman takewa.

Bugu da kari, la'akari da kasa da kaso 4 na tallafin jin kai da ake warewa harkar ilimi a duniya, asusun na UNICEF ya yi kira da a kara mayar da hankali kan samar da ingantaccen ilimi, ta yadda yara da matasa za su samu ilimi cikin yanayi mai aminci, tun daga matakin share fagen shiga firamare har zuwa babbar sakandare, a kasashen dake fama da matsalolin jin kai da rikice-rikice cikin lokaci mai tsawo. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China