Yayin wani taron manema labarai ta kafar bidiyo, ma'aikatar sufurin kasar ta kuma bukaci hukumomi sufurin kasa da na ruwa dake yankin da mahaukaciyar guguwar ta ratsa da su dauki matakan kariya.
Da misalin karfe 5 na yammcin jiya ne mahaukaciyar guguwar ta Mangkhut ta isa gabar birnin Jiangmen na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, kafin daga bisani ta nausa zuwa arewa maso yamma sannan ta shiga jihar Guangxi mai cin gashin kanta ta kabilar Zhuang.
Rahotanni na cewa, kusan dukkan harkokin sufuri sun tsaya cik a gabar biranen dake lardin Guangdomg a jiya Lahadi, kana an rufe manyan hanyoyi dake gabar ruwa. (Ibrahim)