in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a yi bikin ranar tsabta ta duniya a kasar Sin
2018-09-13 21:27:51 cri
Jibi wato ranar 15 ga wata, rana ce ta tsabta ta duniya. A bana, karon farko kasar Sin za ta shirya bikin ranar tsabta ta duniya, don fadakar da jama'ar kasar kan muhimmancin tsabtace muhalli.

Bikin na bana zai samu halartar kamfanoni da kungiyoyi gami da daidaikun mutane wadanda suke maida hankali kan batun shara, da fadakar da miliyoyin jama'a kan batutuwan da suka shafi gano shara, da tsintar shara gami da rage fitar da shara, da kuma yin kira ga jama'a da su gudanar da zaman rayuwarsu mai dorewa.

Ranar tsabta ta duniya ta samo asali ne daga wani aikin kiyaye muhalli a kasar Estonia shekaru goman da suka gabata, inda aka yi kira ga jama'ar kasar da su fita daga cikin gida su tsince gami da kawar da shara da datti dake kewayensu. Yanzu bikin ranar tsabta ta duniya ya riga ya bazu zuwa kasashe 150 na duniya, wanda ya samu halartar masu aikin sa-kai sama da miliyan 165.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China