Kwamitin kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma na kasashen Asiya da Pasifik na Majalisar Dinkin Duniya, da ofishin kula da harkokin hadin-gwiwar kasashe masu tasowa na MDD, gami da ma'aikatar harkokin wajen kasar Thailand su ne suka shirya wannan biki cikin hadin-gwiwa, da nufin murnar cika shekaru arba'in da amincewa da shirin daukar matakai na Buenos Aires, a wajen babban taron hadin-gwiwar kasashe masu tasowa ta fannin fasahohi na MDD.
Da yake jawabi kan hakan, jakadan kasar Sin dake kasar Thailand, Lv Jian ya ce, kamata ya yi kasashe masu tasowa su ci gaba da zurfafa hadin-gwiwarsu, don samar da muhimmin karfi ga ci gaban duk duniya.
Ya ce Sin kasa ce dake taimakawa wajen inganta hadin-gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, wadda ta dade tana nuna goyon-baya, gami da halartar ayyukan hadin-gwiwa tare da sauran kasashe masu tasowa a fannoni daban-daban.(Murtala Zhang)