in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron FOCAC ya haifar da gagarumar nasara inji shugaban Botswana
2018-09-10 10:57:08 cri
Shugaba Mokgweetsi Masisi na kasar Botswana, ya ce ko shakka babu, taron dandalin FOCAC na hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka ya haifar da gagarumar nasara.

Shugaba Mokgweetsi ya bayyana hakan ne ga manema labarai, a filin jiragen sama na birnin Sir Seretse Khama dake fadar mulkin kasar ta Botswana.

Ya ce taron FOCAC na birnin Beijing da ya kammala ba da jimawa ba, kamar taron da aka gudanar a kasar Afirka ta kudu, taron na wannan karo ma ya maida hankali ga tallafin da kasar Sin ke samarwa kasashen nahiyar. Shugaban ya kara da cewa, Sin da Botswana sun amince su kara daga martabar dangantakar su yadda ya kamata.

Shi ma a nasa tsokaci, ministan harkokin waje, da inganta hadin gwiwa na kasar ta Botswana, jinjinawa kasar Sin ya yi, bisa shirya wannan taro da ya hado dukkanin sassan nahiyar Afirka wuri guda, ya kuma baiwa kasashen damar tattauna jigo guda; wato batun samar da ci gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China