180907-Hadin-gwiwar-Sin-da-Afirka-na-samar-da-kariya-ga-muhallin-kasashen-Afirka-luba.m4a
|
A cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin da kasashen Afirka sun samu saurin ci gaban tattalin arzikin kowanensu, kuma kiyaye muhalli yadda ya kamata tare da kiyaye ci gaban tattalin arziki ya zama buri na bai daya a gare su. Kasancewar kasar Sin ta samu wasu kyawawan fasahohi ta fannin bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, kasar Sin da kasashen Afirka kullum suna dora muhimmanci a kan kiyaye muhallin kasashen Afirka a yayin da suke gudanar da hadin gwiwar masana'antu.