180905-Taron-FOCAC-na-Beijing-na-shekarar-2018.m4a
|
An fara taron na FOCAC ne a birnin Beijing na kasar Sin a shekarar 2000, kuma wannan shi ne taro na shida cikin jerin tarukan dandalin, bayan taron koli na dandalin na biyu da ya gudana a nahiyar Afirka a birnin Johannesg na kasar Afirka a shekarar 2015.
Tun lokacin da kasar Sin ta kulla dangantaka da kasashen Afirka, wannan dangantaka take ta bunkasa, abin da ya sa masu sharhi suka bayyana cewa, wannan dangantaka ta yi babban tasiri ga bangarorin biyu, duk da cewa, wasu kasashen yammacin duniya na yi wa wannan kyakkyawar dangantaka bahaguwar fahimta.
Sai dai duk da wannan rashin fahimta da irin wadannan kasashen ke yi wa wannan dangantaka dake tsakanin Sin da Afirka, shugabannin kasar Sin sun jaddada cewa, babban tushen dake tsakanin Sin da Afirka ba zai canja ba.
Alkaluma sun nuna irin tallafi da moriyar da kasashen Afirka suka samu daga wannan dangantaka a bangarori daban-daban kamar su al'adu, ilmi, makamashi, sufuri, tattalin arziki, kiwon lafiya, da dai sauransu. Na baya-bayan nan shi ne shirye-shiryen da kasar Sin ta tsara samar wa nahiyar Afirka da nufin raya masana'antu da bangaren aikin gonanta yayin taron na shekarar 2015. Kuma kasar Sin ta cika alkawarinta na samar da kudin tallafi na dala biliyan 60.
A wannan karo ma kasar Sin ta gabatar da sabbin matakan raya alaka da kasashen Afirka guda 8 da ake fatan aiwatar da su cikin shekaru uku masu zuwa da ma nan gaba, wadanda suka shafi, raya masana'antu, samar da kayayyakin more rayuwa, aikin gona, saukaka harkokin cinikayya da kare muhalli da sauransu.
Saboda muhimmancin wannan dangantaka dake tsakanin bangarorin biyu, ya sa aka kafa wannan dandali, abin dake kara nuna karfafa wannan dangantaka mai tarin alheri ga sassan biyu.
Masu fashin baki na cewa, muddin ana bukatar cin gajiyar wannan dangantaka yadda ya kamata, wajibi ne bangarori biyu su mutunta alkawuran da suka cimma, mutunta juna, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu a bangarori gwamnatoci da al'ummomin kasashen biyu. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)