in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin shige da fice na kasar Sin zai kara zuba jari wajen inganta muhimman ababen more rayuwar jama'a a Afirka
2018-09-04 14:55:49 cri

Shugabar bankin shige da fice na kasar Sin, ko kuma Exim Bank a turance, Madam Hu Xiaolian ta bayyana a wajen taron shugabannin kamfanonin Sin da Afirka karo na shida da aka yi yau Talata a birnin Beijing cewar, bankinta zai kara zuba jari don goyon-bayan kamfanonin kasar Sin wajen gudanar da ayyukan kere-kere da raya ayyukan gona a kasashen Afirka.

Haka kuma, bankin zai samar da tallafin kudade ga kasashen Afirka don su gina yankunan raya masana'antu, da yankunan jigilar kayayyaki, da saukaka matakan hukumar kwastam, da inganta muhimman ababen more rayuwar jama'a da sauransu. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China