180904-Raayoyin-jamian-Najeriya-da-Nijer-game-da-taron-kolin-FOCAC-na-Beijing-na-2018.m4a
|
Barrista Abdullahi Abubakar, shine gwamnan jahar Bauchi a Najeriya, yana daga cikin gwamnonin da suka yi tattaki don halartar taron kolin FOCAC na Beijing, kuma ya bayyana taron da cewa yana da matukar tasiri ga ci gaban kasashen Afrika.
Shi ma Injiniya Sulaiman Adamu ministan albarkatun ruwa na Najeriya, ya ce taron FOCAC wata babbar dama ce ta yin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a matsayinsu na kasashe masu tasowa.
Usman Muhammad, shi ne babban sakataren ofishin hukumar cinikayya ta Jamhuriyar Nijer, ya ce taron kolin dandalin Sin da Afrika taro ne mai muhimmanci dake hada kan shugabannin kasashen Afrika, don tattaunawa da shugabannin kasar Sin, musamman yadda kasar Sin take nuna kauna ga kasashen Afrika, har ma ya bayyana fatan samun kyakkyawar dangantaka tsakanin kasar Sin da Jamhuriyar Nijer da ma kasashen Afrika baki daya.