in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Huldar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka tana kara habaka
2018-09-04 10:53:24 cri

Jiya Litinin da yamma, aka bude taron kolin dandalin FOCAC a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, bisa taken "yin hadin gwiwa domin samun moriyar juna, tare kuma da gina kyakkyawar makoma ga al'ummun Sin da Afirka", inda shugabannin kasashen Afirka da jami'an kungiyoyin kasa da kasa mahalarta taron suka bayyana cewa, sabuwar huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin Sin da Afirka tana kara zurfafa sannu a hankali, kana huldar hadin gwiwa ta sada zumuncin dake tsakanin sassan tana kara habaka.

Tun bayan da aka kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2000, huldar hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu tana kara zurfafa a kai a kai, har ta zama abin koyi ga sauran kasashen duniya yayin da suke gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu da kasashen Afirka, haka kuma ta zama abin koyi ga kasashe masu tasowa yayin da suke gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu.

Yayin taron kolin dandalin da aka gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2015, an sanar da cewa, za a kara kyautata huldar dake tsakanin sassan biyu, har kasar Sin ta gabatar da shirye-shiryen hadin gwiwa guda goma domin raya kasashen Afirka.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa ya bayyana a yayin bikin bude taron na jiya cewa, kawo yanzu an tabbatar da wadannan shirye-shiryen goma, sakamako a jere da aka samu yayin taron kolin Johannesburg suna amfanan al'ummun kasashen Afirka matuka, yana mai cewa, "Shirin hadin gwiwar masana'antun tsakanin Sin da Afirka ya taimaka ga ci gaban masana'antu a yankunan nahihar Afirka, haka kuma ya taimaka wajen kyautata tsarin tattalin arzikin kasashen, shirin hadin gwiwa a fannin zamanintar da aikin gona ya kara karfin kawo albarka a Afirka, shirin hadin gwiwa wajen gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a ya kara karfafa cudanyar dake tsakanin kasashen nahiyar, tabbas wadannan shirye-shirye sun taimake mu a fannoni daban daban kamar kiyaye muhalli da samun dauwamammen ci gaba da kyautata tsarin likitanci da shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan nahiyar Afirka."

Yanzu sabuwar huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin Sin da Afirka tana kara zurfafa sannu a hankali, haka kuma sassan biyu suna gudanar da hadin gwiwa ta sada zumunci lami lafiya. shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU na wannan karo kuma shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya bayyana cewa, kasashen Afirka suna nuna kwazo da himma karkashin laimar shawarar ziri daya da hanya daya domin gudanar da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu da kasar Sin, ko shakka babu hadin gwiwar tana da makoma mai haske, yana mai cewa, "Muna mai da hankali matuka kan cudanyar dake tsakanin kasashen Afirka da kasuwar kasa da kasa, muna fatan kasashen Afirka za su zama muhimmin bangaren cikin hadin gwiwar da ake gudanarwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya."

A matsayinsa na babban bakon da aka gayyata domin ya halarci taron kolin, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta samu babban sakamako mai faranta ran mutanen fadin duniya, kuma tana amfanan sauran kasashe ta hanyar gudanar da hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, kasashen Afirka su ma sun samu babban ci gaba, har wasu kasashen dake nahiyar Afirka sun kasance kasashe mafiya saurin ci gaban tattalin arziki, ana iya cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka tana samar da moriya ga daukacin kasashen duniya, ya ce, "Huldar dake tsakanin Sin da Afirka tana kara karfafa a cikin 'yan shekarun da suka gabata, amincin siyasa da cudanya dake tsakaninsu shi ma ya kara karfafa, lamarin da ya taimakawa yunkurin tabbatar da ajandar samun dauwamammen ci gaba ta MDD nan da shekarar 2030 da ajandar raya kasashen Afirka ta AU nan da shekarar 2063, na yaba da irin wannan hadin gwiwar da ake yi bisa ka'idojin MDD, saboda za ta amfani al'ummun fadin duniya baki daya."

A nasa bangare, shugaban hukumar zartarwar kungiyar AU Moussa Faki ya ce, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka tana da babbar ma'ana wajen kiyaye tsarin gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama, da tsarin cinikayya maras shinge, da kyautata tsarin gudanar da harkokin siyasa da tattalin arzikin kasa da kasa, da kuma kafa sabuwar huldar kasa da kasa da gina kyakkyawar makomar bil Adama, yana mai cewa, "Ina son in jaddada muhimmancin tsarin gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama, kana za mu hada kai tare domin kara kyautata tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China