in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin dandalin FOCAC a birnin Beijing
2018-09-03 22:13:03 cri





A yau Litinin, an bude taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka (FOCAC) a nan birnin Beijing, babban birnin kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin tare da gabatar da muhimmin jawabi, inda ya jaddada cewa, ya kamata Sin da kasashen Afirka su hada kai da juna, domin tabbatar da kyakkyawar makomar Sin da kasashen Afirka ta bai daya, tare da mai da hankali wajen aiwatar da manyan matakai takwas da suka shafi bunkasa masana'antu, da hade ababen more rayuwa, da saukaka harkokin cinikayya, da bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli, ba da inganta kwarewar kasashen, da kiwon lafiya, da musayar al'adu da kuma tsaro.

Taron dai ya kasance sake haduwar shugabannin Sin da kasashen Afirka a nan birnin Beijing bayan tsawon shekaru 12, kuma a sakamakon shigar da kasashen Gambia da Sao Tome and Principe da kuma Burkina Faso dandalin, a yanzu yawan kasashen Afirka mambobin dandali ya kai 53.

A jawabin da ya gabatar a gun bikin bude taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, a sakamakon tarihinsu na kusan daya, da kuma aiki na bai daya da suka sanya gaba, kasar Sin da kasashen Afirka sun gano wata hanyar musamman ta hadin gwiwar samun moriyar juna. Har kullum kasar Sin na hada kan kasashen Afirka bisa ka'idar sahihanci da gaskiya, da akidar "cimma muradu da kuma martaba ka'idoji". Ya ce, "Sin na bin ka'idar gaskiya da zumunci, da zaman daidai wa daida a hadin gwiwarta da kasashen Afirka. Kullum tana mutunta kasashen Afirka da kaunarsu, da kuma nuna musu goyon baya. Ba za ta tsoma baki cikin yadda kasashen Afirka ke kokarin neman samun bunkasuwa ba, kuma ba za ta yi shiga sharo ba shanu cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba. Kana, ba za ta tilastawa kasashen Afirka amincewa da dukkanin ra'ayoyinta ba. Kana kuma, ba za ta gindaya wani sharadin siyasa kan kasashen ba a yayin da take samar masu da tallafi. Haka zalika, kasar Sin ba za ta nemi samun moriya ita kadai ba, yayin da take kokarin zuba jari a kasashen Afirka. Kuma kasar Sin tana fatan kasa da kasa za su mutunta ka'idoji, a yayin da suke kula da harkokinsu da kasashen Afirka."

Shugaban ya ce, yau shekaru uku ke nan da suka wuce, a gun taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC da aka gudanar a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, kasar Sin ta gabatar da manyan shirye-shirye goma na hadin gwiwar Sin da Afirka. Kawo yanzu kuma, an gama gina layukan dogo da na mota da dama, baya ga wasu da har yanzu ake kan ginawa. Baya ga haka, sassan biyu na aiwatar da hadin gwiwa a fannonin kimiyya da ilmi, da kiwon lafiya, da saukaka fatara da sauransu. Kasar ta kuma cika alkawarinta na samar da kudin tallafi na dala biliyan 60.

Xi Jinping ya kara da cewa, al'ummar Sin da kasashen Afirka ne suka fi iya magana a game da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashensu. Ya ce, "Kullum Sin na sanya moriyar al'ummar Sin da kasashen Afirka a gaban komai, kuma tana sa kaimin hadin gwiwar sassan biyu, domin cimma moriyar al'ummarsu. Za mu yi iyakacin kokarin cika alkawuran da muka dauka ga 'yan uwanmu na kasashen Afirka. Kasar Sin na son hada kan kasa da kasa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a nahiyar Afirka. Kasar Sin na maraba da dukkanin abubuwan da za su amfani kasashen Afirka."

Baya ga haka, shugaba Xi Jinping ya kuma gabatar da wasu manyan matakai takwas da za a dauka, wadanda suka shafi bunkasa masana'antu, da ababen more rayuwa, da saukaka harkokin cinikayya da bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli, ba da inganta kwarewar kasashen, da kiwon lafiya, da musayar al'adu da kuma tsaro. A game da saukaka harkokin cinikayya, ya ce,"kasar Sin ta yanke shawarar habaka kayayyaki daga kasashen Afirka, musamman ma kayayyaki da ba na albarkatun kasa ba, kuma tana goyon bayan kasashen na Afirka, wajen halartar bikin baje kolin kasa da kasa a kasar Sin, tare da yafe wa kasashen Afirka da suka fi fama da rashin ci gaba kudin halartar bikin. Tana kuma mara wa kasashen Afirka baya wajen gina yankin ciniki mai 'yanci, kuma za ta ci gaba da tattauna tare da kasashe da shiyyoyi na nahiyar Afirka, wadanda ke da niyyar gudanar da ciniki mai 'yanci."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China