in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#FOCAC#Xi Jinping ya ce Sin za ta kara kyautata ayyukan kiwon lafiya 50 don tallafawa Afirka
2018-09-03 18:04:24 cri
A wajen taron koli na dandalin tattaunwa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC wanda ake yi a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, Sin ta yanke shawarar kar inganta wasu ayyukan kiwon lafiya guda hamsin don tallafawa kasashen Afirka, da bada tallafi don gina hedikwatar cibiyar shawo kan cututtuka ta Afirka, da asibitocin karfafa zumunta tsakanin Sin da Afirka da sauran wasu muhimman ayyuka. Sin za ta aiwatar da ayyukan hadin-gwiwa tare da kasashen Afirka ta fannin kiwon lafiya, musamman ma ayyukan da suka shafi shawo kan cututtuka masu yaduwa, da cutar Sida, da cutar malariya da sauransu. Sin za ta kara horas da wasu kwararrun likitoci ga kasashen Afirka, da ci gaba da turawa gami da inganta kwarewar likitocin da za su je Afirka don bada tallafi. Kasar Sin za ta kara gudanar da ayyukan tallafawa mutanen Afirka wadanda ke fama da cututtukan da suka shafi idanu da baki da sauransu. Har wa yau, Sin za ta aiwatar da ayyukan kiwon lafiya don tallafawa mutane marasa karfi, musamman ma mata da yara. (Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China