in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cika shekaru biyu da fara zirga-zirgar layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna
2018-08-29 14:31:39 cri


A ranar 26 ga watan Yulin shekara ta 2016, aka kaddamar da layin dogo tsakanin Abuja fadar mulkin tarayyar Najeriya zuwa Kaduna dake arewacin kasar, wanda wani kamfanin kasar Sin mai suna CCECC ya dauki nauyin gina shi. Layin dogon ya kasance irinsa na zamani na farko a Najeriya, kasa ce data fi kowace kasa yawan al'umma a nahiyar Afirka, kana, layin dogo na farko a nahiyar Afirka wanda kamfanin kasar Sin ya gina bisa ma'aunin Sin. A wajen bikin kaddamar da aikin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, kaddamar da layin dogon ya dace da babban burin gwamnatinsa wato kawo sauye-sauye ga kasar, a wani kokari na kara samar da sauki ga zaman rayuwar jama'ar Najeriya ta hanyar inganta muhimman ababen more rayuwar al'umma.

A watan Agustar shekara ta 2006, gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirinta na zamanintar da layukan dogon kasar a cikin shekaru 25. A watan Oktobar shekarar, kamfanin CCECC da gwamnatin Najeriya sun daddale wata yarjejeniya, inda ya dauki nauyin gudanar da ayyukan shimfida wani layin dogon, wanda ya tashi daga birnin Ikko, cibiyar tattalin arziki dake kudancin Najeriya, ya ratsa ta Abuja, a karshe ya kai birnin Kano dake arewacin kasar. Tsawon wannan layin dogo ya kai kilomita 1315.

Amma bayan da aka daddale yarjejeniyar, sakamakon wasu dalilan da suka shafi sauyin gwamnatoci da karancin kudade, aka dakatar da wannan gagarumin aiki. Domin sassauta matsalar da gwamnatin Najeriya ta fuskanta ta karancin kudade, gwamnatin kasar Sin ta samar mata da rancen kudi mai sassaucin kudin ruwa, a wani kokari na gudanar da ayyukan shimfida layin dogon mataki mataki.

A matsayin mataki na farko na layin dogo tsakanin Ikko zuwa Kano, layin dogon da aka shimfida tsakanin Abuja da Kaduna yana da tsawon kilomita 186.5, mai kunshe da tashoshi tara, kana, yawan kudin da aka zuba a wannan aiki ya kai kimanin dala miliyan 850. A watan Fabrairun shekara ta 2011, an kaddamar da aikin gina layin dogo tsakanin Abuja zuwa Kaduna, daga baya a ranar 1 ga watan Disambar shekara ta 2014, aka kammala aikin shimfida shi, wanda ya kasance layin dogon zamani na farko a nahiyar Afirka wanda aka gina shi ta hanyar amfani da fasahohion kasar Sin kuma bisa ma'aunin kasar.

A halin yanzu, akwai fasinjojin Najeriya da yawa wadanda suka yi zirga-zirga ta wannan layin dogo. Wani dan kasuwa mai suna Mustapha Idriss ya nuna babban yabo ga layin dogon zamani tsakanin Abuja zuwa Kaduna inda ya ce, idan babu tsarin zirga-zirgar jiragen kasa mai kyau a kasa, sam ba zata cimma burinta na neman bunkasuwa ba. Layukan dogo na da matukar muhimmanci ga kasar, wanda yana taimakawa Najeriya wajen samun ci gaba.

Shi ma a nasa bangaren, manajan kula da harkokin zirga-zirgar layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna na babban kamfanin jiragen kasa na Najeriya, Victor Adamu cewa ya yi, a halin yanzu a kowace rana, adadin yawan fasinjojin da suke yin zirga-zirga a layin dogon ya zarce dubu uku, wanda yawansu ke karuwa a kowace rana.

Bisa alkaluman da babban kamfanin jiragen kasa na Najeriya ya fitar, an ce, bayan da aka fara zirga-zirgar layin dogon, ya zuwa yanzu, gaba daya akwai fasinjojin kusan miliyan daya wadanda suka yi zirga-zirga. Kuma irin wannan nasara da aka samu ta kara baiwa gwamnatin Najeriya kwarin-gwiwar bisa fasahohin kasar Sin. A watan Maris din shekara ta 2017, an fara aikin shimfida layin dogo tsakanin Ikko zuwa Ibadan, kana kuma an riga an rattaba hannu kan yarjejeniyar shimfida layin dogo tsakanin Ibadan zuwa Kano.

Dalilan da suka sa layin dogon zamani tsakanin Abuja zuwa Kaduna ke kara samun karbuwa sosai a Najeriya sune saboda yana da matukar tsaro, da tafiya cikin natsuwa, kana da tafiya akan lokaci. Wani babban jami'i a babban kamfanin jiragen kasa na Najeriya ya bayyana cewa, daya daga cikin nasarorin da layin dogon ya samu shine, ya yi zirga-zirga na tsawon shekaru biyu ba tare da samun hadari ko daya ba, abun dake da alaka sosai da fasahohin kamfanin CCECC.

Haka zalika, a halin yanzu, kamfanin CCECC na kasar Sin na ci gaba da horas da ma'aikata 'yan Najeriya don inganta kwarewarsu wajen kula da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna. A nasa bangaren, mataimakin babban manajan kamfanin CCECC reshen Najeriya, Mista Qian Hongxiang ya ce, Najeriya tana bukatar kamfaninsa ya ci gaba da samar da goyon-baya har zuwa lokacin da Najeriya zata samu kwararrun ma'aikata wadanda ke da kwarewa sosai wajen tafiyar da harkokin zirga-zirgar jiragen kasan.

Bugu da kari kuma, yayin da yake gudanar da ayyukan shimfida layin dogo a Najeriya, kamfanin CCECC na kokarin samar da taimako don kyautata zaman rayuwar al'umma a kewayen layin dogon, ciki har da gina makarantu, da hanyoyin mota da samar da kyautar na'urorin aikin jinya da dai sauransu, wadan nan al'amuran sun samu matukar yabo daga jama'ar Najeriya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China