180829-Ranar-agajin-jin-kai-ta-duniya.m4a
|
MDD ce ta kebe ranar 19 watan Agustan kowace shekara don wannan rana mai muhimmanci da ma'aikatanta ke kaiwa ga rasa rayukansu yayin taimakawa wadanda ke neman agajin gaggawa sakamakon tashin hankali, fadace-fadace ko wani bala;I daga indallahi.
An fara gudanar da wannan shiri ne a karshen karni na 19. Taron kolin kasa da kasa na farko kan agajin jin kai shi ne wanda aka gudanar ranakun 23 da 24 ga watan
Mayun shekarar 2016 a Istambul na kaszar Turkiya. Taron da tsohon babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya shirya, wanda kuma ya hallara gwamnatoci da kungoyin fararen hula da masu zaman kansu da masu ba da agajin jin kai.
Abubuwan da aka tattauna yayin taron sun hada da hanyoyin kawo karshen tashin hankali da yadda za a daidaita matsalar idan ta taso da ma kudaden tallafin jin kai.
Alkaluman MDD na nuna cewa, ma'aikatanta da ma jami'an bada agaji 313 ne rikici ya rutsa da su cikin mabambantan hare-hare 158 a fadin kasashe 22 a bara. Daga cikin wannan adadi, 139 ne aka kashe, adadin da ya karu idan aka kwatanta da 107 na shekarar 2016.
Bayanai na nuna cewa, an kai 2 bisa 3 na hare-haren ne a kasashe 5 kadai, da suka hada da Sudan ta Kudu da Syria da Afghanistan da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma Nijeriya.
Ranar bada agaji ta duniya ta bana, na da muhimmanci matuka, bisa la'akari da cewa a bana ne ake cika shekaru 15 da harin da aka kai birnin Bagadazan kasar Iraki, wanda ya yi sanadin mutuwar jami'an MDD 22, haka zalika a bana ne ake cika shekaru 11 da harin da aka kai birnin Algiers na kasar Aljeriya da ya yi sanadin mutuwar ma'aikatan MDD 17.
Masu fashin baki na cewa, wajibi ne a rika martaba da kare rayukan ma'aikatan dake samar da agaji ga fararen hula da suka jikkata sakamakon tashin hankali ko yake-yake ko kuma bala'I daga indallahi. (Saminu, Fa'iza, Ibrahim/Sanusi Chen)