A yayin da ake kokarin zurfafa hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, a waje guda kuma sassan biyu na ta karfafa hadin kai a fannin al'adu. A yau, za mu kawo muku wani bayani ne game da wata matashiya 'yar kasar Afirka ta kudu, wadda ta yi karatu a birnin Beijing na kasar Sin.