in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Thomas Thabane: Sin sahihiyar aminiyar Afrika ce
2018-08-23 11:36:22 cri

Firaministan kasar Lesotho Thomas Thabane ya shaidawa taron manema labarai a Masero, babban birnin kasar, gabanin bude taron kolin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika na Beijing cewa, Sin sahihiyar aminiyar Afrika ce.

Thomas Thabane ya bayyana cewa, taron da za a kira wata alama ce a tarihin dangantakar Sin da Afrika, dake bayyana niyyar Sin ta taimakawa nahiyar Afrika ta fuskar tattalin arziki, da inganta rayuwar jama'ar Afrika.

Ya kuma bayyana cewa, Sin ta cika alkawarinta na baiwa Lesotho taimako, inda ta gina makarantar sada zumunta tsakanin Sin da Lesotho da babban dakin littattafai da Sin ta ba da taimako wajen gina su, da kuma ginin majalisar dokoki da rukunin masana'antu.

Ya kara da cewa, taimakon da Sin take baiwa Afrika, taimako ne da ke shafar dukkanin nahiyar, ba wata kasa kadai a Afrika ba.

Ban da wannan kuma, Thomas Thabane ya nuna cewa, baya ga goyon bayan da Sin ke baiwa Afrika ta fuskar tattalin arziki, tana kuma goyon bayan kasashen Afrika a harkokin kasa da kasa, da kungiyoyin kasa da kasa misali MDD, inda Sin ta kan goyi bayan al'ummar Afrika. Wannan ya sa, ko shakka babu Lesotho tana tare da kasar Sin a duk lokaci da take bukatar taimakonta. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China