in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantakar ciniki tsakanin Sin da Japan na bunkasuwa mai inganci
2018-08-17 15:37:38 cri

Sin da Japan ba su iya rabuwa da juna ba a cikin shekaru 40 da suka gabata, tun lokacin da suka kulla dangantakar diplomasiyya, musamman ma a fannin ciniki da tattalin arziki.

Kayayyakin kirar kasar Sin, wata alama ce ta rahusa da inganta ga babbar kasuwanni, da sha'anin sayar da abinci na kasar Japan. A sa'i daya kuma, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai dorewa, ta baiwa kamfanonin Japan babbar dama, tare da kawo amfani da tsare-tsaren da kamfanonin Japan za su tsayar nan gaba.

Ban da wannan kuma, Sin na da rinjaye mai karfi ta fuskar na'urori masu sarrafa kansu, da hada-hadar kudi ta sadarwar Intanet da dai sauransu. A nata bangare Japan ita ma tana da rinjaye, da fasahohin zamani a fannin kera kananan na'urorin lantarki, da bada kulawa ga tsoffi, da ba da jiyya da sauransu, abubuwan dake samar da zarafi mai yakini ga daga matsayin hadin gwiwar Sin da Japan ta fuskar ciniki da tattalin arziki. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China