
An fara yin amfani da tasha ta farko dake iya sarrafa shara mafi girma a Beijing a ranar 16 ga wata, wadda take zaune a kusa da tsaunin Baiwangshan dake yankin Haidian. Tana da na'ura mai inganci da take iya sarrafa shara mafi girma wadda ta kai ton 10 a ko wace rana, ciki hadda katifa, sofa da sauransu. Za a kafa irin wannan tasha guda 9 a yankin a cikin wannan shekara. (Amina Xu)