Dukkanin fasinjojin dake cikin jirgin su 281 sun sauka lafiya lau ba tare da samun raunuka ba. Hukumomi suna cigaba da gudanar da bincike game da jirgin a wani karamin filin jirgin sama dake Chania, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Girika AMNA ya rawaito.
Jirgin saman samfurin Boeing 753 na kamfamnin jirgin saman Condor ya tashi ne daga Hurghada zuwa Dusseldorf.
A labarin da wata jaridar cikin gidan kasar "Proto Thema" ta wallafa, an tsinci wata takardar gargadin ne dake nuna yiwuwar kaddamar da harin bom a cikin bandakin jirgin inda aka rubuta kalmar "bomb" a jikin takardar. Nan take aka raka jirgin zuwa filin jirgin saman Girka inda wasu kananan jiragen sojin saman Girka biyu suka yiwa jirgin rakiyar.
Kamfanin dillancin labaran na AMNA yace, an tura wasu kwararrun masana kwance bom da kwararrun karnuka masu sansano ababen fashewa domin bincike a wajen.