in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta musanta biyan kudin fansa ga Boko Haram don sako 'yan matan sakandaren Dapchi
2018-08-17 10:16:44 cri
A jiya Alhamis gwamnatin Najeriya ta jaddada matsayinta cewa sam bata biya kudaden fansa ga mayakan kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram ba domin neman a saki 'yan matan sakandaren garin Dapchi su sama da 100 wadanda aka yi garkuwa dasu a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Ministan yada labarai da raya al'adu na Najeriya Lai Mohammed, yace gwamnatin kasar tana kalubalantar duk wani mutum ko wata kungiyar dasu gabatar da hujja dake tabbatar da cewa gwamnatin ta biya wasu kudade domin neman a sako 'yan matan.

A wani rahoton da MDD ta fitar ta yi ikirarin cewa gwamnatin Najeriyar ta biya wasu makudan kudade a matsayin fansa ga 'yan Boko Haram da nufin sako 'yan matan sakadaren na Dapchi a jahar Yobe a ranar 19 ga watan Fabrairu.

Mayakan Boko Haram sun sako 'yan matan da suka yi garkuwa dasu ne bayan shafe wata guda, bayan da gwamnatin Najeriyar ta tabbatar da cewa ta tattauna da kungiyar domin neman a saki 'yan matan.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua Lai Muhammad yace, "Ko kadan ba zai gamsar ba a yi ikirari cewa Najeriya ta biya kudin fansa, ko da kadan ne ko kuma masu yawa. Dole ne a samu wata kwakkwarar hujja dake tabbatar da wannan ikirarin".

Jami'in yayi watsi da ikirarin da MDDr ta yi, inda ta bayyana shi da cewa "karya ce tsagwaronta" sai dai idan har MDDr zata iya bayar da wata hujja kwakkwara dake tabbatar da cewa kasar ta biya kudaden.

An sako dukkan 'yan matan sakandaren na Dapchi da sauran wadanda Boko Haram din ta yi garkuwa dasu ne, biyowa bayan tattaunawar da aka gudanar tsakanin wasu kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka yi hadin gwiwa da gwamnatin Najeriya, kamar yadda jami'an gwamnatin suka tabbatar da hakan a watan Maris.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China