An yi hasashen cewa, adadin yawan waken soya da za'a girbe a bana a Amurka, zai kai ton miliyan 120, wanda shi ne matsayin koli a tarihi. Haka kuma hasashen ya ce, yawan waken soya da za'a ajiye a bana, zai karu da kashi 80 bisa dari, idan aka kwatanta da na bara.
Har wa yau, ma'aikatar ayyukan gonan Amurka, ta daga hasashen da ta yi game da yawan masara da za'a girbe a duk fadin kasar a bana, wanda zai kai matsayi na uku a tarihi.
Sin babbar kasa ce ta farko da take shigo da waken soya daga Amurka, wato a kowace shekara, sulusin yawan waken soya da Amurkar ke fitarwa ana shigar da shi ne cikin kasar Sin. Amma gwamnatin kasar Amurka ta sanar da cewa, za ta sanya kudin fito na kashi 25 bisa dari kan kayayyakin da za ta shigar kasar ta daga Sin, masu darajar dala biliyan 50.
Daga baya gwamnatin Sin ta maida martani da kara sanya kudin fito ga waken soya da za ta shigo da shi daga Amurka.
Manazarta na ganin cewa, akwai rashin sanin tabbas game da makomar zaman rayuwar manoman Amurka. Saboda a watanni da dama da suka gabata, kasar Sin ta riga ta kara yawan waken soya da take ajiyewa a cikin kasar, kuma za ta kara shigo da waken daga kasar Brazil a nan gaba. Duk da cewa Turai ta yi alkawarin kara shigar da waken soya daga Amurka, amma sam ba za ta maye gurbin kasar Sin ba.(Murtala Zhang)